Majalisa Ta 10: Cikakken Jerin Sunayen Tsaffin Sanatoci 72 Da Suka Buƙaci A Tsayar Da Akpabio Da Barau

Majalisa Ta 10: Cikakken Jerin Sunayen Tsaffin Sanatoci 72 Da Suka Buƙaci A Tsayar Da Akpabio Da Barau

  • Tsofaffin sanatoci 72 sun nuna goyon bayansu ga Godswill Akpabio ya riƙe matsayin shugaban majalisar dattawan ta goma
  • Sanatocin sun kuma goyi bayan a bawa sanatan Kano ta arewa Barau Jubril Maliya kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan
  • Tsofaffin sanatocin sun ce domin tabbatar da adalci da kuma fatan samun ci gaba a ƙasa ne ta sanya suka ga dacewar a bawa wani daga kudu maso kudu ya shugabanci majalisar

Abuja - A daidai lokacin da ake ta batun shigabancin majalisar dokoki ta 10, gungun tsofaffin sanatoci guda 72 sun nuna goyon bayan su ga tsohon ministan Naija-Delta wato Godswill Akpabio.

Dama dai a ƙarshen makon nan an jiyo gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya na shelanta ma duniya cewa ya na ganin Akpabio ne zai jagoranci majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

Har An Soma Zargin Tinubu da Rashin Adalci Tun Kafin Hawa Mulki Kan Takarar Majalisa

Akpabio Barau
Akpabio da Barau I. Jibrin. Hoto: Business Day
Asali: UGC

Sai dai Leadership ta ruwaito cewa wani tsagi na tsofaffin sanatocin da ke bayan wani ɗan takarar sun nesanta kansu daga goyon bayan Akpabio sannan kuma suka caccaki masu goyon bayan.

Mun yi hakan domin tabbatar da adalci da cigaba

Basheer Lado, tsohon sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya bayyana ma manema labarai a madadin sauran sanatocin cewa sun goyi bayan a miƙa kujerar shugabancin majalisar dattawan zuwa yankin kudu maso kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lado ya ce bayan tattaunawa a tsakanin su da kuma sauran masu ruwa da tsaki, sun cimma matsaya kan cewar a miƙa shugabancin majalisar dattawan zuwa kudu maso kudu don tabbatar da daidaito da adalci.

Ya kuma ƙara da cewa kujerar shugaban majalisar dattawa ita ce kujera ta uku mafi girma a tsarin shugabancin Najeriya wacce kuma take da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da ayyuka na ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Ya ƙara da cewar abu ne mai muhimmanci ace duk wanda ke riƙe da wannan kujera yana da goyon bayan jam'iyyar shi da kuma na abokan aiki wanda kuma sun duba sunga Akpabio ya haɗa waɗannan abubuwa.

Har yanzu Akpabio bai nuna sha'awar tsayawa takarar ba

Lado ya ƙara da cewar duk dai don ganin an tabbatar da adalci da daidaito, sun yanke shawarar marawa Sanatan da ke wakiltar Kano ta arewa, Barau I. Jubril baya a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Sai dai duk da wannan goyon bayan da ya ke samu daga mambobin jam'iyyar shi ta APC, har yanzu Godswill Akpabio bai nuna aniyar shi ba ta neman kujerar shugabancin majalisar dattawan.

Ga cikakken jerin sunayen tsofaffin sanatocin da suka nuna goyon bayan su ga Akpabio:

  1. Ben Ayade
  2. George Akume
  3. Basheer Lado
  4. Rilwan Akanbi
  5. Barnabas Gemade​​​​
  6. Grace Bent
  7. Binta Masi Garba
  8. Ayogu Eze
  9. Andy Uba
  10. Ibrahim Ida
  11. Olorunnimbe Mamora​​
  12. Anthony Adeniyi​​​
  13. Ganiyu Solomon​​​
  14. Gbenga Obadara​​​
  15. Gbenga Kaka​​​
  16. Musiliu Obanikoro​​​
  17. Arise Ayo​​​​
  18. Felix Kolawole Bajomo​​
  19. Hassain Mudashiru​​​
  20. Domingo Obende​​​
  21. Wilson Ake​​​​
  22. Ita Enang​​​​
  23. Heineken Lokpobiri​​
  24. Clever Ikisikpo
  25. Ita Giwa
  26. Ibrahim Musa​​​
  27. Alex Kadiri​​​​
  28. Ocheja Emma Dangana
  29. Jibriu Wowo
  30. Isa Maina
  31. Mohammed Ohiare​​
  32. Abubakar Sodangi
  33. Joseph Akaagerger​​
  34. Jack Tilley Gyado​​​
  35. Abubakar Tutare​​​
  36. Bello Tukur​​​​
  37. Ahmed Barata​​​​
  38. Abba Aji​​​​​
  39. Mohammed A. Mohammed​​
  40. Umar Idris​​​​​
  41. Adamu Talba​​​​
  42. Sidi Ali​​​​​
  43. Timothy Adudu​​​​
  44. Ishaq Adebayo Salman​​​
  45. Akin Odunsi​​​​​
  46. Seye Ogunlewe​​​​​
  47. Fatima Raji Rasaki​​​
  48. Lanre Tejuoso​​​​
  49. Nkechi Nwaogu​​​​
  50. Margery Chuba Okadigbo
  51. Mohammed Saleh​​​
  52. Sani Kanba​​​​​
  53. Abubakar Abdullahi Naamo​​
  54. Danladi Sankara
  55. Mohammed Ibrahim​
  56. Sola Adeyeye
  57. Anthony Agbo​​​
  58. Ikechukwu Obior
  59. Chris Adighije​​​
  60. Emma Anosike​​​​
  61. Jalo Zarami
  62. Alkali Jajere
  63. Oladipo Odujinrin
  64. Mohammed Alkali
  65. Sunday Ogbuoji
  66. Abu Ibrahim
  67. Bello Maitama
  68. Saddiq Yar’adua
  69. Jide Omoworare
  70. Anthony Manzo
  71. Aminu Inuwa
  72. Magnus Abeh

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa 2 Sun Janye Daga Takarar Shugaban Majalisar Dattawa, Sun Koma Bayan Wani

Wani rahoto da Vanguard ta samu da yammacin ranar Litinin na nuni da cewa kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun aminta da zabin da tsofaffin sanatocin 72 suka yi.

Jam'iyyun adawa na yunkurin tsaida dan takara a majalisa

Jam'iyyun adawa dai sun sha alwashin cewa za su yi amfani da barakar da ke neman kunno kai cikin jam'iyyar APC wajen tsayar da nasu dan takarar.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 10 ne 'yan jam'iyyar APC suka nuna ra'ayinsu kan neman kujerar kakakin majalisar wakilan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel