'Aljanna Na Ke Son Shiga': Matashi Ya Bankawa Kansa Wuta a Kano, An Jefa Shi a Ruwa
- Wani matashi a Kano ya jefa al'ummar wata unguwa cikin tashin hankali bayan ya bankawa kansa wuta
- Matashin mai suna Suleiman Muntari ya kona kansa ne a titin Panshekara da ke jihar Kano
- Shaidu sun ce matashin ya zuba fetur a jikinsa, ya kunna wuta, alhali mutane na zaton wasa yake yi har ya kama da wuta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya bayan matashi ya kona kansa da hakan ya yi ajalinsa nan take.
An ce matashin mai suna Suleiman Muntari ya banka wa kansa wuta a kan titin Panshekara da ke jihar wanda lamarin ya daga hankulan mutane da ke yankin.

Asali: Original
Kalaman matashin kafin ya kona kansa
A cewar Tribune, Sulaiman ya zuba fetur a jikinsa sannan ya kunna wuta, yana ikirarin cewa yana son zuwa 'Aljanna'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi suka ce an yi kokarin ceto shi daga lamarin amma wutar ta riga ta ci jikinsa.
“Ya ce yana son zuwa Aljanna, mutane sun dauka wasa yake yi, amma kafin wani ya hana shi, ya riga ya zuba fetur sannan ya kunna wuta.
"Cikin dan kankanin lokaci, wuta ta riga ta kama shi."
- Cewar wani Saminu Isah
Zargin da ake yi wa matashin a Kano
Wasu mazauna yankin sun ce ana zargin matashin mai suna Sulaiman yana cikin maye ne, domin yana rikice tare da furta kalamai marasa ma’ana kafin faruwar lamarin.
“Ba a cikin hayyacinsa yake ba. Za ka ji warin wani abu mai karfi daga jikinsa, kuma yana tangal-tangal yana ihu da furta abubuwa marasa ma’ana."
- Cewar wata Aisha Salisu

Asali: Facebook
Yadda mutanen Kano suka yi kokarin ceto shi
Yayin da abin ke faruwa, mutane dake kusa sun yi kokarin taimaka masa, har ma wata majiya ta ce an jefa shi a ruwa amma wutar da riga ta yi masa illa.
Aisha ta kara da cewa:
“Mutane sun firgita suka gudu, wasu sun kokarta sun zuba masa ruwa, amma lokaci ya kure."
Wasu mazauna unguwar sun yi kokarin cetonsa ta hanyar ja shi cikin wata magudanar ruwa kusa da wurin, amma wutar ta riga ta yi barna sosai.
“Kamar fim din ban tsoro ne. Wasu samari sun kokarta su taimaka masa ta hanyar jan shi cikin ruwa, amma wutar ba ta tsaya ba. Fatar jikinsa ta fara fita."
- Cewar wani, Ibrahim Jafar
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin da ya faru.
Mahaifi ya yi ajalin ƴarsa a Kano
Mun ba ku labarin cewa al'umma sun shiga tashin hankali da wani magidanci ya hallaka ƴarsa yayin wata ƴar hatsaniya da ta auku a tsakaninsu a cikin gida.
An ce magidancin ya hallaka ƴar tasa ne sakamakon bugun da ya yi da wani abu a kanta wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta.
Majiyoyi sun ce jami'an ƴan sanda sun yi gaggawar zuwa wajen da lamarin ya auku domin fara gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng