Zazzafar Suka Ta Tilastawa Tinubu Dakatar da Azumin Rokon Allah Ya Wadata ’Yan Najeriya da Abinci

Zazzafar Suka Ta Tilastawa Tinubu Dakatar da Azumin Rokon Allah Ya Wadata ’Yan Najeriya da Abinci

  • Ma’aikatar noma ta dakatar da yunkurinta na yin azumi da addu’a domin samar da abinci da kashe yunwa a Najeriya
  • An sanar da za a yi taron neman taimakon Allah wajen samarwa ‘yan Najeriya abinci da habaka fannin a kasar
  • Sai dai, ‘yan Najeriya na yiwa gwamnati Kallon lusara wajen kama hanyar addu’a a matsayin tashi tsaye sai Allah ya taimake ta

Abuja A ranar Asabar, 14 ga Yuni, 2025, Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya ta dakatar da shirin gudanar da azumi da addu’o’i na kwanaki uku da ta tsara domin neman taimakon Allah wajen fuskantar matsalar yunwa da Rashin abinci a Najeriya.

Tun da farko, wata takardar da ta yi yawo a kafafen sada zumunta ta nuna cewa an umurci duka ma’aikatan ma’aikatar da su halarci zaman addu’a a ranar 16, 23 da 30 ga watan Yuni, a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja.

Gwamnati ta fasa azumin yaki da yunwa
An fasa azumin yaki da yunwa a Najeriya | Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Sai dai kwatsam, a cikin wata sabuwar sanarwa da ta fito daga ma’aikatar, an sanar da dage shirin ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

An dage taron addu’a saboda bakin ‘yan Najeriya?

Wannan matakin ya biyo bayan sukar da jama’a da kafafen yada labarai suka yi wa shirin, inda da dama ke tuhumar dacewar irin wannan mataki a daidai lokacin da yunwa da hauhawar farashin kayayyaki ke addabar 'yan kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar farko wacce Daraktar kula da Ma’aikata, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu, ta bukaci ma’aikatan da su yi azumi da addu’a karkashin shirin da aka lakaba masa suna “Divine Intervention for Protection and National Development”.

A cewar takardar:

"An gayyaci duka ma’aikatan Ma’aikatar Noma da Abinci ta Tarayya zuwa zaman addu’a na musamman, domin neman jagorancin Allah da tallafa wa kokarin gwamnati na cimma isasshen abinci a kasa.”

Daga baya, a wata sabuwar sanarwa da ta fito daga daraktar, an bayyana cewa an dage shirin zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba, ba tare da an bayyana dalili ba.

Sukar da jama’a suka yi ya tilasta dage taron

Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa matakin dage shirin ba zai rasa nasaba da yadda jama’a da kafafen yada labarai suka caccaki shirin ba.

Jama’a da dama na kallonsa a matsayin sakaci da lusaranci a daidai lokacin da gwamnati ke bukatar daukar matakan zahiri don magance matsalolin tattalin arziki da yunwa.

Hangen masu sharhi

Masu sharhi da dama sun bayyana damuwarsu, suna cewa kamata ya yi ma’aikatar ta mayar da hankali kan hanyoyin kirkira da tsarin bunkasa noma, samar da iri, taki da horar da manoma, maimakon dogaro da addu’a a matsayin mafita ga matsalolin abinci.

A halin yanzu, ba a fitar da sabuwar rana da za a gudanar da shirin ba, kuma ba a bayyana ko za a aikata hakan ba nan gaba.

Legit.ng Hausa za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da kawo muku sabbin bayanai dangane da yadda ma’aikatar za ta fuskanci kalubalen abinci a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.