Lokaci Ya Yi: Shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya a Plateau Ya Kwanta Dama

Lokaci Ya Yi: Shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya a Plateau Ya Kwanta Dama

  • Shugaban kungiyar CAN na jihar Filato, Rev. Fr. Polycarp Lubo, ya rasu a wani asibiti da ke Jos bayan gajeriyar rashin lafiya
  • An ce Lubo ya kamu da rashin lafiya ne bayan wani hadari da ya rutsa da shi makon da ya gabata a Jos
  • Wani Rabaran a Jos ya fitar da sanarwar ta'aziyya inda ya mika sakon jaje ga iyalansa da kuma mabiya addinin Kirista

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - An sanar da rasuwar, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Rabaran Fasto, Polycarp Lubo, ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya da ake zargin hakan ya faru bayan hatsarin mota da ta rutsa da shi.

Shugaban Kiristoci a ya rasu a Arewa
Shugaban ƙungiyar Kiristoci a Plateau ya rasu. Hoto: Prince Sekat Sabo.
Asali: Facebook

Punch ta samu labarin cewa Lubo ya rasu ne da safiyar Lahadi 15 ga watan Yunin 2025 a wani asibiti da ba a bayyana ba da ke Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Gwamna Mutfwang ya ce kan Lubo

Mutuwar na watanni kadan bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya taya marigayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

A watan Nuwamban da ya gabata, Gwamna Barista Caleb Manasseh Mutfwang, ya yaba wa Lubo game da kokarin wanzar da zaman lafiya.

Hakan na cikin wata sanarwa ta taya murna da daraktan yada labaransa, Gyang Bere, ya sa wa hannu.

Mutfwang ya yabawa rawar da Polycarp Lubo ke takawa wajen samar da hadin kai da lafiya a cikin coci, jihar da ma wajenta.

An yi rashin shugaban Kiristoci a Arewa
Shugaban ƙungiyar Kiristoci a Plateau ya rasu . Hoto: Polycarp Lubo.
Asali: Twitter

Sanadin mutuwar marigayi, Polycarp Lubo a Plateau

Hakan ya faru bayan gajeriyar rashin lafiya da ta biyo bayan wani hadari da ya faru da shi makon da ya gabata, cewar rahoton Vanguard.

Mutuwarsa ta samu karin tabbaci ta cikin wata sanarwar ta’aziyya da Sakatare Janar na cocin na Katolika da ke Jos, Daniel Gyang, ya sanya wa hannu.

Sanarwar mai taken, “Sanarwar Mutuwa,” ta yi ta’aziyya ga iyalan Lubo, kungiyar CAN ta jihar Filato, da kuma sauran shugabannin addini da limaman Katolika.

Sanarwar ta ce:

“A cikin jimami da mika wuya ga ikon Allah, muna sanar da rasuwar Rabaran Dr. Polycarp Lubo, wanda ya koma ga Ubangiji da safiyar Lahadi 15 ga Yuni, 2025.
“Muna jajanta wa iyalansa, CAN na jihar Filato, limaman cocin Jos, mabiya cocin St. William da ke Zawan da dukkan mabiya addinin Katolika.
“Allah ya jikansa da rahama, da dukkan sauran muminan da suka rigamu gida gaskiya, amin.”

Babban Fasto a Arewa, Azzaman ya bar duniya

Mun ba ku labarin cewa Kiristoci sun shiga jimami bayan rasuwar fitaccen Fasto, Ayuba Azzaman David, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa Kaduna daga jihar Benue.

Abokinsa, Fasto Mohammed Mohammed Bishara ne ya tabbatar da rasuwar a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, inda ya ce an yi babban rashi tare da nuna alhininsa kan haka.

Bishara ya yabawa irin gudunmawar Azzaman wajen wa’azi, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa ya sa ya huta cikin rahama da salama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.