Kungiyar CAN Ta Fusata Kan Hare-hare a Arewa, Ta Jagoranci Zanga-zanga Don Nuna Bacin Ranta

Kungiyar CAN Ta Fusata Kan Hare-hare a Arewa, Ta Jagoranci Zanga-zanga Don Nuna Bacin Ranta

  • Shugaban kungiyar CAN a jihar Plateau, Rabaran Polycarp Lubo ya jagoranci zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar
  • Kungiyar reshen jihar ta dauki matakin ne don nuna rashin jin dadi kan hare-haren da ya ki ci ya ki cinyewa a fadin jihar
  • Hakan ya biyo bayan hallaka mutane fiye da 200 da 'yan bindiga suka yi a karshen watan Disambar 2023 a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) a yanzu haka ta na jagorantar zanga-zanga a Jos da ke jihar Plateau.

Kungiyar reshen jihar ta dauki matakin ne don nuna rashin jin dadi kan hare-haren da ya ki ci ya ki cinyewa a fadin jihar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Atoni-janar a jihar Arewa ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 81

Kungiyar CAN ta jagoranci zanga-zanga a Jos kan hare-haren 'yan bindiga
Kungiyar CAN dauki matakin ne don nuna rashin jin dadi game da hare-haren. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Mene dalilin daukar matakin Kungiyar CAN?

Shugaban kungiyar a jihar, Rabaran Polycarp Lubo shi ke jagorantar zanga-zangar tare da shugaban ECWA, Rabaran Dakta Stephen Baba Panya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da shugaban majami'ar COCIN, Rabaran Dakta Amos Mohzo da shugaban cocin Methodist, Rabaran Nkechi Nwosu da sauran shugabannin Kiristoci a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan hare-haren bindiga da ya addabi jihar musamman a yankunan karkara, Punch ta tattaro.

'Yan sanda sun cafke wasu mutane a Plateau

A ranar jajiberin Kirsimeti, mahara sun hallaka mutane fiye da 200 a wani kauye da ke jihar wanda ya ta da hankula matuka a kasar.

Masu zanga-zangar sun fara tattakin ne daga shatatalen PRTVC inda suka nufi gidan gwamnatin jihar don nuna rashin jin dadinsu kan hare-haren.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta sanar da cafke wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a kai harin na watan Disamba, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

"Ba zama": Gwamnan jihar Arewa ya yi ganawar sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an gano dalili

Kakakin rundunar a jihar, Alfred Alabo ya ce an samu zaman lafiya a yankin da aka kai harin bayan cafke mutanen.

'Yan sanda sun cafke kwararriyar mai satar waya

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da cafke wata mata da ta kware a satar waya a birnin Maiduguri.

Matar mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' ta shiga hannu ne da wasu mutane 84 a jihar.

Matar ta bayyana yadda ta ke satar wayar tata cikin hikima ba tare da an ankara da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel