'Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Basarake a Kaduna, an Tafka Barna

'Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Basarake a Kaduna, an Tafka Barna

  • Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a garin Doka Avong da ke cikin ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna
  • Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matar Hakimin garin Doka Avong tare da ɗansa a yayin harin da suka kai
  • Harin da ƴan bindigan suka kai ya jawo fargaba da tashin hankali a zukatan mutanen yankin waɗanda suka nemi hukumomi su kawo musu ɗauki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun yi awon gaba ba da matar wani basarake da ɗansa a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace mutanen ne a wani hari da suka kai hari a garin Doka Avong da ke cikin gundumar Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kai farmaki a fadar basarake a Kaduna
'Yan sun sace matar basarake a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin wanda aka kai a daren ranar Asabar, 14 ga watan Yunin 2025, ya jefa mazauna garin Doka Avong cikin firgici da tashin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun farmaki fada

A cewar wani rahoto na hukuma da aka gabatar wa Sarkin Kufana, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da gungun ƴan bindiga da dama suka mamaye gidan Hakimin Doka Avong.

Maharan sun yi garkuwa da matar Hakimin, wadda aka bayyana da suna Deborah Jonah mai shekaru 38, da kuma ɗansa Maxwell Jonah mai shekaru 14.

An tabbatar da wannan abin takaici ne cikin wata wasiƙa da Mr. Stephen Maikori, mai kula da gundumar Kufana, ya sanya wa hannu.

“Wannan lamari mai ban tausayi ya jefa al’ummar cikin tsananin fargaba da tashin hankali."
“A bisa haka, ina kira cikin girmamawa ga hukumomin tsaro da su hanzarta ɗaukar matakan da suka dace domin ƙara sa ido da ƙarfafa tsaro a Doka Avong da gundumar Kufana gaba daya."

- Mr. Stephen Maikori

Ya ƙara jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da na ƙarfi domin hana sake faruwar irin wannan lamari da kuma kare rayuka da dukiyoyi, da kuma dawo da ƙwarin gwiwa cikin zukatan jama'a.

Sace matar da ɗan Hakimin ya ƙara tsananta fargabar rashin tsaro a Kajuru, wacce ta sha fama da hare-haren ƴan ta’adda a cikin ƴan shekarun nan.

'Yan bindiga sun sace matar basarake a Kaduna
'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar basarake a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

A halin da ake ciki, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.

Sai dai manyan shugabannin al’umma na ci gaba da yin kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su tura jami’ansu cikin gaggawa domin dakile yuwuwar ƙarin hare-hare a yankin.

Jami'an tsaro sun samu nasara kan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasara kan miyagun ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Jami'an tsaro sun samu nasarar ceto wasu fasinjoji da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi a ƙaramar hukumar Zurmi.

Ƴan bindigan sun dai yi awon gaba da fasinjojin ne bayan da suka tare motocinsu lokacin da suke tafiya a kan hanyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng