Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga, an Ceto Fasinjojin da Aka Sace

Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga, an Ceto Fasinjojin da Aka Sace

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile wani mugun nufi da ƴan bindiga suka shirya kan wasu fasinjoji a jihar Zamfara
  • Wasu miyagun ƴan bindiga dai sun tare hanya a ƙaramar hukumar Moriki inda suka yi awon gaba da fasinjoji
  • Jami'an tsaro sun maida martani cikin gaggawa inda suka ceto guda bakwai daga cikinsu yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Jami'an tsaro a jihar Zamfara sun samu nasarar ceto fasinjoji bakwai da ƴan bindiga suka sace.

Jami'an tsaron sun ceto mutanen da ƴan bindigan suka sace ne a hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi, a cikin yankin Moriki na ƙaramar hukumar Zurmi.

Jami'an tsaro sun ceto fasinjoji a Zamfara
Jami'an tsaro sun ceto fasinjojin da aka sace a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun tare hanya a Zamfara

Majiyoyin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Juma'a, 13 ga watan Yuni, lokacin da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka tare babban titin a Kwanar Boko, inda suka kai hari kan motoci masu ɗauke da fasinjoji.

Bayan tare hanyar, ƴan bindigan sun farmaki motocin haya da ke tafiya a hanyar, inda suka sace wasu fasinjoji da ba a san yawansu ba a lokacin.

Ana zargin cewa ƴan bindigan sun yi amfani da muggan makamai da manyan bindigu a lokacin harin, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin firgici.

Da jami’an tsaro suka samu rahoton faruwar lamarin, sai suka ƙaddamar da aikin sintiri tare da yi wa dazukan da ke kewaye da yankin ƙawanya.

A yayin wannan aikin, jami’an tsaro sun yi nasarar gano da kuma ceto mutane bakwai daga hannun masu garkuwa da mutane da suka haɗa da maza huɗu da mata uku, dukkansu cikin ƙoshin lafiya.

Bayan an ceto su, an ɗauke su zuwa ofishin ƴan sanda da ke Moriki domin ba su kulawar gaggawa da jin bayaninsu a cikin natsuwa.

Bayan haka ne za a miƙa su ga iyalansu don komawa gida cikin aminci.

'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Zamfara
Jami'an tsaro sun ceto fasinjoji a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An ba buƙaci jama'a su ba da bayanai

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da ke hannun ƴan bindigan

A cewar wata majiya daga rundunar tsaro, an ƙara ƙaimi wajen bincike da sintiri a dazukan yankin don zakulo sauran fasinjojin da aka sace da kuma cafke masu laifin.

Hukumomin tsaro sun buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani don taimakawa a yaƙi da matsalar garkuwa da mutane da ta addabi yankin.

Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a wani wurin da sojoji suke zama a jihar Benue.

Miyagun ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro na rundunar tsaron Benue da ke aiki a wurin a lokacin da suka kai harin.

Daga baya dakarun sojoji sun kawo ɗauki inda suka fatattaki ƴan bindigan tare da ƙwato babura a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng