Jami'an Tsaro Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka

Jami'an Tsaro Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a juhsr Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a wani wurin da sojoji ke zama a ƙaramar hukumar Katsina-Ala
  • Duk da samu nasarar daƙile harin da aka yi, ƴan bindigan sun hallaka jami'ai biyu na rundunar tsaron jihar Benue

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Ƴan bindiga sun kai hari kan wani wurin da sojoji ke zama a Tor-Donga, ƙaramar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

Aƙalla jami’ai biyu na rundunar tsaron jihar Benue (BSCPG) sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka jikkata a sakamakon harin da ƴan bindigan suka kai.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Benue
Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga a Benue Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hari a Benue

Wata majiya ta bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare lokacin da wasu ƴan bindiga kusan 10, waɗanda ke kan babura guda biyar, suka dirar wa wurin da sojoji ke zama.

Ƴan bindigan sun dirar wa wurin da sojojin ke zama ne a Tor-Donga da nufin ƙaddamar da hari kan dakarun da ke aiki a wurin.

Jami’an BSCPG da ke bakin aiki a lokacin ne suka fuskanci ƴan bindigan domin daƙile harin.

A yayin musayar wuta da aka yi, wani daga cikin jami’an tsaron, wanda aka gano da suna Torna Atim, ya samu harbin bindiga kuma ya rasu nan take.

Wani jami’i mai suna Fanga Gundepuun kuwa, ya samu harbin bindiga a ƙafarsa kuma daga baya ya rasu a asibiti.

Sauran jami’ai uku, wato Guusu Terver, Mzuuga Terzungwe da Abugh Ivanbee, dukkansu mazauna ƙauyen Tor-Donga ne, sun samu raunuka iri-iri.

Nan take aka garzaya da su zuwa asibitin Nguher da ke Katsina-Ala domin samun kulawa ta gaggawa.

Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga

Bayan aukuwar harin, dakarun sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka isa wurin da sauri kuma suka fatattaki ƴan bindigan.

Ƴan bindigan sun tsere zuwa cikin daji, inda suka bar babura guda biyu a wurin da aka yi musayar wutar.

Sojoji sun fattaki 'yan bindiga
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wannan ya nuna cewa sojojin da sauran jami’an tsaron sun mayar da martani cikin ƙwarewa da sauri domin hana mummunar ɓarna.

A halin yanzu dai, an kwashe baburan guda biyu da aka bari a wurin harin zuwa hannun hukumomi domin gudanar da bincike.

Har yanzu hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike tare da farautar waɗanda suka kawo harin domin tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban doka.

Ƴan bindiga sun kai hari a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai munanan hare-haren ta'addanci a jihar Benue.

Ƴan bindigan sun ƙaddamar da hare-haren ne a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Apa da Gwer ta Yamma na jihar Benue.

Munanan hare-haren da ƴan bindigan suka kai sun yi sanadiyyyar rasuwar aƙalla mutane sama da 40 yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng