Karatun Karshe da Sheikh Abubakar Giro Argungun Ya Yi Kafin Ya Komawa Allah

Karatun Karshe da Sheikh Abubakar Giro Argungun Ya Yi Kafin Ya Komawa Allah

  • Abubakar Giro Argungu ya gabatar da karatun tafsirin Al-Kur’ani har ana gobe zai bar duniya
  • A karshen karatun, an yi sallama da nufin malamin musuluncin zai cigaba da darasi washegeri
  • Malamin ya karar da lokacin rayuwarsa wajen karantar da addini da gwagwarmaya a Najeriya

Kebbi - Ana saura sa’o’i kadan ya bar Duniya, Abubakar Giro Argungun ya gudanar da darasin tafsiri watau ilmin ma’anonin Kur’ani.

Abubakar Giro Argungun ya yi karatun ne a ranar 5 ga watan Satumba 2023 wanda ya zo daidai da Talata, 21 ga watan Safar 1445.

Kamar yadda wani mai suna IZALA ya wallafa bidiyo a shafinsa na X watau Twitter, a karshen karatun ne ya amsa tambayoyin jama’a.

Abubakar Giro Argungu
Sheikh Abubakar Giro Argungun Hoto: www.hausaloaded.com
Asali: UGC

Falalar zikiri bayan sallah - Gero

Malamin ya yi magana a kan muhimmancin zikirori da ake yi bayan sallolin farilla a musulunci, ba da dadewa ba sai aka ji labari ya cika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘La ilaha illal Lah wahdahu la sharika Lahu, Lahul Mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kullu shai’in Qadir'

Marigayi Giro Argungu ya ambato hadisi a game da falalar addu’ar da ake yi a ranar Arafah, ya ce hakan ya zo a littatafan hajji da umrah.

A cewar malamin addini, babu addu’ar da Ubangiji Sarki (SAW) yake so kamar wanda aka yi a lokacin tsayuwar Arafah a watan Zul Hajj.

Giro Argungu zai cigaba da karatu a gobe

Shehin yake cewa a zikirin babu inda aka ambaci bukatar duniya illa neman albarkacin Ubangiji wanda aka tsarkake tare da ba Shi girma.

An kammala karatun ne da nufin za a cigaba zuwa Laraba, a yammacin ranar ne malamin ya rasu.

Hakan ya faru bayan babban malamin ya yi fama da ciwon da ya yi sanaddiyar da ya yi doguwar jinya a asibitin kasar waje kafin ya warke.

Afuwar Abubakar Giro Argungu

A shekarar bara aka rahoto Shiekh Abubakar Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya a kan wani bidiyonsa da yake yawo a Najeriya.

Fai-fan ya nuna malamin yana kakkausan kalamai kan "makiya" Shugaba Muhammadu Buhari, daga baya ya ce ba haka yake nufi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel