Kotun Musulunci Ta Illata Masoya, Ta Hana Saurayi Zuwa Unguwarsu Budurwarsa

Kotun Musulunci Ta Illata Masoya, Ta Hana Saurayi Zuwa Unguwarsu Budurwarsa

  • Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rigasa ta hana wani matashi suna Salisu Salele kusantar tsohuwar budurwarsa, Bilkisu Lawal
  • Mai shari’a Salisu Abubakar-Tureta ya ce daga yau, Salisu ba zai kira ko gana da Bilkisu ba, kuma haramun ne ya bi unguwarsu
  • Salisu ya ce yana son Bilkisu amma ba zai iya aure yanzu ba har sai bayan shekaru biyu, domin yana karatu kuma bai da kudin sadaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rigasa a jihar Kaduna, ta raba soyayyar wasu masoya guda biyu bayan korafin iyayen budurwa.

Kotun ta haramtawa Salisu Salele zuwa kusa da ko wata alaƙa da Bilkisu Lawal bisa kin amincewar iyayensu saboda wasu dalilai.

Kotu ta raba masoya a Kaduna
Kotun Musulunci ta yanke hukunci mai tsauri kan masoya a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gargadin kotu ga wasu masoya a Kaduna

Alkalin kotun, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya yanke hukunci bayan masoyan sun amince su rabu da juna a gaban iyayensu da shugaban unguwa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce daga ranar da aka yanke hukuncin, Salisu ba zai kuma zuwa layinsu Bilkisu ba ko hira ko kuma ya kira ta a waya wanda yin hakan zai jawo wa kansa fushin hukuma.

Alkalin ya ce:

“Daga yau, Salisu ba zai kira ko gana da Bilkisu ba, an hana shi bin unguwarsu ko tsayawa kusa da gidan su Bilkisu.
“Idan an kama shi yana kiranta ko ganinta a ko’ina, za a dauki matakin da ya dace a kansa."
Kotu ta raba rayuwar masoya bayan korafin iyayensu
Kotun Musulunci ta haramtawa saurayi kusantar budurwarsa. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Musabbabin shigar da korafi da iyayen suka yi

Majiyoyi sun ce mahaifiyar Bilkisu, Raliya Lawal, ce ta shigar da kara a kotu tana neman a tilasta auren saurayin da budurwar.

“Muna zaune a unguwa daya, kuma yana zuwa wajen diyata ba tare da amincewar mu ba a matsayin iyayenta.

“Na kai kukana ga mahaifiyarsa, sai ta ce dansu bai shirya aure ba yanzu.
"Salisu ya daina zuwa wajen diyata, amma yana kiranta a waya, yana rokon ganawa da ita a wasu wurare, ba na so ya bata tarbiyyar da na baiwa diyata, don haka na garzaya kotu."

- Cewar Raliya

Martanin saurayi bayan raba shi da budurwarsa

A jawabinsa, Salisu ya ce yana sonta, amma ba zai iya aure ba har sai bayan shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce:

“Ni dalibi ne a jami’ar tarayya, kuma bana son aure ya dauke min hankali, bugu da kari, ban da kudin sadaki,

Matashin ya tabbatarwa da kotu cewa har yanzu yana tare da iyayensa ba tare da matsala ba.

Budurwa ta yanka masoyinta a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa wata kotun Majistare a Kaduna ta gurfanar da Abigail Victor mai shekara 23 bisa zargin caka wa saurayinta wuka saboda zargin yaudara.

Lauyan gwamnati ya ce Abigail ta hada kai da wasu mutane biyu da suka tsere da lakada wa Dominic James duka tare da caka masa wuka.

Alkalin kotun ya bayar da belinta kan N200,000 da wanda zai tsaya mata, wanda dole ne ya zama cikin ‘yan uwanta da ke biyan haraji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.