Mokwa: Tinubu da Sauran Ƴan Siyasa da Suka ba da Gudunmawa Sanadin Ambaliyar Ruwa

Mokwa: Tinubu da Sauran Ƴan Siyasa da Suka ba da Gudunmawa Sanadin Ambaliyar Ruwa

Shugaban kasa, Bola Tinubu da sauran gwamnoni sun jajantawa gwamnatin jihar Niger kan iftila'in ambaliyar ruwa a Mokwa inda suka ba da gudunmawa mai tsoka.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Mokwa, Niger - A karshen watan Mayun 2025 aka samu iftila'in ambaliyar ruwa a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Niger.

Lamarin ya tayar da hankalin mutane da kuma hukumomi duba da asarar rayuka da aka tafka sanadin iftila'in.

An samu iftila'in ambaliyar ruwa a Niger
Tinubu da mutane da gwamnoni da suka tallafa a ambaliyar ruwa a Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Asali: Facebook

Ambaliyar ruwa: Gudunmawar da aka samu

Rahoton Punch ya ce akalla mutane fiye da 500 suka rasu sanadin iftila'in wanda har yanzu ana ci gaba da gano gawarwaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin iftila'in, hukumomi, gwamnatoci da kuma gidauniyoyi da kungiyoyi sun ba da gudunmawa mai tsoka domin rage radadin da ake ciki.

Daga cikin gudunmawar da aka bayar akwai na kudi, kayan sakawa, kayan abinci da sauransu.

Legit Hausa ta duba wadanda suka ba da gudunmawa sanadin ambaliyar da ta afku a jihar Niger.

1. Bola Tinubu

An tabbatar da cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba da gudunmawa mai tsoka yayin jaje zuwa garin Mokwa.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya wakilci Tinubu inda ya nuna damuwa kan abin da ya faru.

Daga bisani, Tinubu ta bakin Shettima ya ce mai gidansa a madadin gwamnatin tarayya ya ba da N2bn.

Tinubu ya jajanta kan ambaliyar ruwa a Niger
Tinubu ya tallafa da N2bn sanadin ambaliyar ruwa a Niger. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

2. Gwamna Umaru Bago (Niger)

Gwamna Mohammed Umaru Bago na Niger ya bayar da tallafin N1bn ga waɗanda ambaliya ta shafa a Karamar Hukumar Mokwa da ke cikin jihar.

Haka kuma, gwamnan ya ba da gudunmawar motoci 50 cike da nau’ikan hatsi domin rage wa waɗanda ambaliyar ta shafa ƙuncin rayuwa.

Har ila yau, ya sanar da bayar da kwangilar gina titin Mokwa zuwa Rabba da kuma gadoji uku a kan hanyar, a kan kuɗi N7bn.

3. Gwamna Babagana Umara Zulum (Borno)

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya je ziyarar jaje sanadin ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Niger.

Zulum bayan yi wa gwamnati ta'aziyya ya kuma ba da gudunmawar N300m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Gwamnan jihar Niger, Umaru Bago, ya yaba bisa gudunmawar da Zulum ya ba da, inda ya sha alwashin cewa za a yi amfani da su yadda ya dace.

Zulum ya mika sakon jaje kan ambaliyar ruwa a Niger
Zulum ya tallafa da N300m kan ambaliyar ruwa a Niger. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

4. Gwamna Agbu Kefas (Taraba)

Gwamnatin Jihar Taraba ta mika sakon ta’aziyyarta ga gwamnatin da al’ummar Jihar Niger sakamakon mummunar ambaliya da ta afku.

Wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Sanata mai wakiltar Taraba ta Tsakiya, Manu Haruna, ta jajanta wa Gwamna Umaru Bago kan wannan masifa.

Yayin ziyarar, Sanata Haruna ya isar da ta’aziyyar gwamnatin Jihar Taraba, inda ya bayyana cewa gwamnati tana cikin jimamin al’ummar Niger, musamman waɗanda ambaliyar ta shafa kai tsaye.

Ya bayyana cewa gwamnan ya bayar da tallafin N50m a madadin gwamnatin Jihar Taraba domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

4. Peter Obi

A bangarensa, tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya ba da gudunmawar N20m, cewar rahoton The Guardian.

Obi wanda ya yi tattaki har garin Mokwa inda ya jajanta abin da ya faru tare da ba al'ummar yankin hakuri.

Obi ya kadu bayan ambaliyar ruwa a Niger
Peter Obi ya ba da gudunmawar N20m a Niger. Hoto: Peter Obi.
Asali: Facebook

5. Sanata Abubakar Sani Bello

Sanata Abubakar Sani Bello ya ba da tallafin N50m domin rage radadin ambaliyar da ta hallaka mutane da lalata gidaje a jihar Niger.

Tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin Adamu Usman ta wakilci tsohon gwamnan wajen isar da sakon ta’aziyya da kuma ba da tallafin.

Sarkin Mokwa ya gode matuƙa bisa gudunmawar, yana mai cewa ambaliyar ta zo wa mutane a ba-zata, kuma ta jawo babbar asara.

Har ila yau, gamayyar yan majalisun jihar Niger sun ba da tallafin N20m da kungiyoyi da kuma gidauniyoyi da dama.

Niger: Buhari ya jajanta kan ambaliyar ruwa

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa kan mutuwar mutane fiye da 100 sakamakon ambaliya a Niger.

Muhammadu Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyya kan hadarin mota da ya hallaka ‘yan wasa da jagororinsu 22 a jihar Kano.

Ya bayyana cewa aukuwar wadannan abubuwa a lokaci guda ya girgiza shi matuka, yana fata da addu'ar samun sauƙi ga wadanda suka jikkata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.