Hakeem Baba Ahmed Ya Sake Dura kan Gwamnatin Shugaba Tinubu

Hakeem Baba Ahmed Ya Sake Dura kan Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana kan gwamnatin Bola Tinubu
  • Tsohon hadimin na Tinubu ya bayyana cewa shugaban ƙasan da ya shiga ofis a Mayun 2023 ya gaza inganta rayuwar ƴan Najeriya
  • Ya buƙace shi da ya tashi tsaye domin tabbatar da cewa ana samar da ingantaccen mulki a dukkan matakan gwamnati da ake da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kasa inganta rayuwar talakawan Najeriya da kuma samar da ingantaccen shugabanci.

Hakeem Baba-Ahmed ya ragargaji Tinubu
Hakeem Baba Ahmed ya soki gwamnatin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed
Asali: Facebook

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Political Paradigm' na tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakeem Baba-Ahmed ya soki Bola Tinubu

"Babu shakka, gwamnatin Tinubu ta kasa cika tsammanin cewa za ta kawo sauyi mai inganci a harkar shugabanci."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed, wanda kuma shi ne tsohon mai magana da yawun ƙungiyar dattawan Arewa, ya bayyana cewa cire tallafin fetur da gwamnatin Tinubu ta aiwatar ya shafi rayuwar talakawa sosai.

Ya ce, ko da yake ba za a iya sa ran shugaban ƙasa zai dawo da tallafin fetur ba, ya kamata ya magance ɓarnar da ke faruwa a matakin jihohi da ƙananan hukumomi kan kuɗin da aka samu bayan cire tallafin.

An ba Shugaba Tinubu shawara

Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya ɗauki matakai wajen bin diddigi kan shugabanci a dukkan matakan mulki guda uku, tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya kuma buƙaci shugaban ƙasa da ya tunkari cin hanci da rashawa da matsalar tsaro, rage talauci, da kuma mayar da hankali kan samar da ababen more rayuwa da suka shafi cigaban al'umma da jin daɗin jama'a.

Tsohon hadimin na Tinubu ya kuma buƙace shi da ya tabbatar da cewa ana amfani da ƙudaden da ake tura wa gwamnoni, musamman na jam’iyyar APC yadda ya kamata.

"Akwai yawan asara, yawan cin hanci da rashawa da kuma ɓarna ta albarkatu da ke faruwa."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba Ahmed ya soki gwamnatin Tinubu
Hakeem Baba Ahmed ya ce Tinubu ya gaza inganta rayuwar 'yan Najeriya Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Asali: Twitter

Baba-Ahmed ya ce ana samun ci baya

Tsohon mai magana da yawun ACF ya ce dukkan shugabannin da suka mulki Najeriya tun daga shekarar 1999 suna ƙara taɓarɓarewa fiye da waɗanda suka gabace su.

"Najeriya na cikin wani hali. Duk da cewa muna da tsarin dimokuradiyya, babban abin da ya kamata ya zama ginshiƙi ya ɓace."
"Wannan kuwa shi ne ra'ayin cewa mutane na zaɓar shugabanni ne don su yi musu hidima, kare dukiyarsu, da amfani da albarkatunsu wajen gina kasa mai amfani ga ƴan ƙasa."

- Hakeem Baba-Ahmed

Shugaba Tinubu ya ba Wike shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da kalamai kan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ministan da ya toshe kunnuwansa daga masu sukar ayyukan da yake yi a birnin Abuja.

Mai girma Bola Tinubu ya kuma yabawa ministan kan irin ayyukan ci gaba da yake gudanarwa, inda ya ce shi shugaba ne mai hangen nesa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng