Bam Ya Tashi da Mutane ana tsaka da Shagalin Babbar Sallah a Jihar Sakkwato

Bam Ya Tashi da Mutane ana tsaka da Shagalin Babbar Sallah a Jihar Sakkwato

  • An rasa rayukan bayin Allah da wani bam ya tashi da mutane a yankin ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato
  • Rahotanni sun nuna cewa mutane sun mutu, wasu uku sun samu raunuka sakamakon tashin bam din ranar Lahadi da ta gabata
  • Har yanzu rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba amma gwamnatin ƙaramar hukumar Tangaza ta tabbatar da faruwar lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Wani bam ƙirar cikin gida ya tashi da mutane a ranar yawon sallah na biyu a jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Akalla mutane shida aka tabbatar da sun mutu da bom ɗin ya tarwatse a kauyen Gwabro da ke karamar hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.

Bam ya tashi a Sakkwato.
Mutane 6 sun rasa rayukansu da bam ya tashi ranar yawon sallah a Sakkwato Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar Lahadi yayin da musulmin Najeriya ke ci gaba da bukukuwan Sallah Babba (Eid-el-Kabir).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mutane suka taka bam a Sakkwato

Bayanai sun nuna cewa mutanen da abin ya shafa na kan hanya daga kauyen Gwabro zuwa garin Zurmuku da ke makwaftaka da su, lokacin da suka taka bam ɗin bisa rashin sani.

Mutum shida sun rasa rayukansu sakamakon tashin bam din, yayin da wasu uku kuma suka samu raunuka.

Sai dai, hukumar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin har kawo yanzu.

Gwamnatin Tangaza ta tabbatar da lamarin

Alhaji Garzali Raka, mai ba da shawara kan harkokin tsaro ga karamar hukumar Tangaza, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa tuni aka riga aka yi wa dukkan wadanda suka mutu jana'iza bisa tsarin addinin Musulunci.

“Wannan abu ne mai matukar tayar da hankali. Muna kokari sosai wajen tallafawa wadanda suka jikkata da kuma tabbatar da tsaro a yankin,” in ji shi.

Rahotanni sun ce fashewar bam ɗin ta faru ne a kusa da wani sansanin jami'an tsaro da ke wajen kauyen Zurmuku.

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato.
Hukumomi sun bukaci mutane su rika sa ido kan masu shige da fice a yankunansu a Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Ana zargin Lakurawa ne suka dasa bam

Ana zargin cewa ‘yan ta'addan ƙungiyar Lakurawa, wadanda ke addabar wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi, ne suka dasa bam ɗin.

Wadanda suka jikkata, mata guda uku sun samu raunuka masu tsanani, kuma an garzaya da su zuwa asibiti a Tangaza domin ba su kulawa.

Hukumomin sun bukaci jama’a da su zama masu lura da abin da ke faruwa a muhallinsu, su kuma rika kai rahoton duk wani motsi da ba su aminta da shi ba ga hukumomin tsaro.

Haka kuma, an bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen sintiri da yaki da ayyukan ta’addanci a yankin, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Sojoji ragargaji ƴan ta'adda a Sokoto, Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ƙara samun nasara a yaƙi da matsalolin tsaro a jihohin Sakkwato da Zamfara.

Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun lalata sansaninin yan ta'adda lokacin da suka ka samame cikin dazuka a jihohin guda biyu.

Dakarun sojoji sun kutsa wurare masu hatsari da suka haɗa da Gidan Madi, ƙauyen Tsamiya, Tudun Ruwa, Alela, da wasu jeji da ƴan bindiga ke ɓuya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262