"Tsarin Tinubu Ya Zo da Alheri," An Ji Abin da Ya Jawo Man Fetur Ya Yi Araha a Najeriya
- Attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce tsarin sayen ɗanyen mai da Naira ne makasudin rage farashin man fetur a Najeriya
- Ɗangote ya bayyana cewa wannan tsari yana daga cikin waɗanda suka fi tasiri daga tsare-tsaren da gwamnatin Shugaba Tinubu ta zo da su
- Shugabsn Ɗangote Group ya kuma yabawa sabon tsarin da Shugaba Tinubu ya kawo na amfani da kayayyakin mu na cikin gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙara yabawa tsarin sayen ɗanyen mai da Naira, wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da shi.
Attajirin ɗan kasuwar ya ce wannan tsarin shi ne maƙasudin rage farashin litar man fetur da matatar man feturinsa ke yi akai-akai.

Asali: Twitter
Abin ke sa matatar Ɗangote rage tsadar fetur
Ɗangote ya ce tsarin da gwamnatin Bola Tinubu ta ɓullo da shi na hada-hadar ɗanyen mai da Naira yana taimaka wa matatarsa wajen wadatar da fetur a kasa, The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da Shugaba Tinubu ya kai ziyara matatar Dangote, inda kuma ya ƙaddamar da aikin gyaran hanyar tashar jiragen ruwa daga Epe zuwa Ijebu-Ode.
Ɗangote ya ce:
“Ɗaya daga cikin tsare-tsaren da suka yi tasiri daga cikin manufofin wannan gwamnati shi ne tsarin sayen ɗanyen mai da Naira.
"Wannan tsari ya ƙara tabbatar da aniyar wannan gwamnati wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa."
'Farashin fetur a Najeriya ya fi araha'
Alhaji Aliko Ɗangote ya ƙara da cewa wannan tsari ya ba su damar rage farashin kayayyakin mai kamar, fetur, dizal, man jirgin sama (Jet A1), gas da sauransu.
“Har yanzu wasu na ganin fetur da ake sayar da kowace lita kasa da ₦900 ya yi tsada, amma babu inda fetur ke ƙasa da $1, wanda ya kai kusan ₦1,600 a yanzu s yammacin Afirka,” in ji shi.
Dangote ya kuma yaba da manufar "Nigeria First" da gwamnatin Tinubu ta sake ɓullo da shi, wadda zai mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin cikin gida maimakon na ƙetare.

Asali: Getty Images
Ɗangote ya yabawa sabon tsarin Najeriya a farko
“Manufar nan ta ‘Najeriya ce a farko,’ ta dace da burin mu a kamfanin Dangote, wato samar da abin da muke amfani da shi domin kasarmu ta zauna da gindinta tare da rage dogaro da ƙasashen waje."
A ƙarshe, Dangote ya ce wannan ci gaba yana taimakawa matuƙa wajen daidaita darajar Naira da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, rahoton Leadership.
Tsarin sayar da danyen mai da Naira ya fara aiki ne a hukumance ranar 1 ga Oktoba, 2024, bayan da majalisar zartarwa ta Tarayya ta amince da bayan umarnin Shugaba Tinubu.
Kamfanoni 6 sauke farashin man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanonin da ke dillancin man fetur guda shida a Najeriya sun rage farashin man fetur a Najeriya.
Wasu daga cikin dilolin sun rage farashi daga N903 zuwa N827, yayin da wasu suka rage kudin kowane lita daga N869 zuwa N868.
Ana sa ran Matatar Dangote za ta sake rage farashin man da take fitarwa daga tasharta, wanda yanzu haka ya tsaya a kan N825.
Asali: Legit.ng