Dilolin Mai Sun Rage Farashin Man Fetur ana Gobe Sallah a Najeriya
- Kamfanoni shida da ke rarraba man fetur sun rage farashi domin janyo abokan ciniki yayin da gasa ke ƙaruwa a kasuwancin mai
- Wasu daga cikin dilolin sun rage farashi daga N903 zuwa N827, yayin da wasu suka rage kudin kowane lita daga N869 zuwa N868
- Ana sa ran farashin zai ci gaba da sauka, musamman idan darajar gangan danyen mai a duniya ya ci gaba da kasancewa a ƙasa da $70
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanonin rarraba man fetur shida a Najeriya sun rage farashin man fetur, lamarin da ke nuna yadda gasa ke ƙaruwa a tsakanin masu kasuwancin man fetur.
Matatun da suka rage farashin sun haɗa da Emadeb, First Royal, MENJ, Aiteo, Pinnacle da Hyde, kuma rage farashin ya faru ne a jiya kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Asali: Getty Images
Rahotan Vanguard ya nuna cewa wannan sauyi a farashin na da alaƙa da ƙoƙarin kamfanonin wajen jawo kwastomomi, ganin yadda man fetur ke yawaita a cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda diloli suka rage farashin man fetur
Kamfanin Emadeb ya rage farashin lita daga N903 zuwa N827, yayin da First Royal ya saukar da shi daga N828 zuwa N826.
A daya bangaren, MENJ ya rage farashi daga N827 zuwa N826, Aiteo kuma daga N826 zuwa N825, Pinnacle daga N856 zuwa N850, sai Hyde daga N869 zuwa N868.
Wani masani a harkar man fetur ya bayyana cewa farashin na iya ci gaba da raguwa, duba da farashin gangar danyen mai da ke kan $65 a kasuwar duniya.
Ya kuma ce ana sa ran Matatar Dangote za ta sake rage farashin man da take fitarwa daga tasharta, wanda yanzu haka ya tsaya a kan N825.
Dalilin sauke farashin man fetur a Najeriya
Shugaban ƙungiyar masu sayar da man fetur ta PETROAN, Dr Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa rage farashin da matatun suka yi na da nasaba da gasa mai ƙarfi a kasuwar cikin gida.
Rahoton Economic Confidential ya nuna cewa Dr Gillis-Harry ya ce:
“Wannan rage farashin na nuna yadda masu shigo da mai ke ƙoƙarin daidaita kasuwarsu, domin idan ba su rage ba, ba za su iya sayar da man a cikin gida yadda ya kamata ba.”
Ya ƙara da cewa gasa tana da amfani, amma idan ta yi yawa fiye da kima, hakan na iya zama barazana ga ci gaban bangaren kasuwancin man fetur.
Saukin farashin na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke kara kokawa kan tsadar rayuwa da tashin farashin kayan masarufi.

Asali: Getty Images
Gidajen mai da ake samun feturin Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta fitar da sanarwa game da rage farashin man fetur a Najeriya.
Bayan tabbatar da rage farashin man fetur, matatar Dangote ta jero gidajen mai shida a fadin Najeriya da 'yan kasa za su samu fetur a farashi mai rahusa.
Matatar Dangote ta bayyana gidajen mai din ne domin tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun samu damar sayen fetur mai sauki.
Asali: Legit.ng