Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci

Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci

  • An kafa dokokin kayyade kayan aure a wata Masarauta dake jihar Jigawa
  • Daga cikin dokokin an hana yin 'Gara' kuma lefe kada ya wuce N100,000
  • Hakazalika an hana yin taro irinsu Kauye Day, Arabian Night, dss

Jigawa - Masarautar Gumel ta kafa sabbin dokokin kayyade kayan aure a yankinta domin saukakawa matasa aure sakamakon halin da al'umma ke fama da shi.

A takardar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar kuma Maji Dadin Gumel, Alhaji Murtala Aliyu, an umurci Limaman Juma'ar Masarautar su fadakar da al'umma kan wannan sabuwar doka.

Masarautar tace ta kafa dokokin ne domin saukake wahalhalu da tsada da al'adu dake tattare da lamuran daurin aure.

Ga hoton wasikar:

Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci
Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci Hoto: Arewa Radio
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

Dokoki nawa ne aka kafa?

A kwafin dokokin da masarautar ta hadawa Limaman, an ga jerin dokokin 19 da suka bayyana abubuwan da ya kamata Saurayi mai niyyar aure ya tanada.

Daga cikin Masarautar ta lissafa adadin abubuwan mutum zai saya da kuma abubuwan da ba zai saya ba.

Hakazlika an hana wasu tsare-tsare da bukukuwa da aka saba yi irinsu ranar Kauyawa da sauransu.

Ga jerin dokokin:

Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci
Masarautar Gumel ta kafa dokar kayyade kayan aure, ta umurci Limamai su sanar a Masallaci
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel