Kano: An Cafke Matasa da ke Bidiyo domin 'Trending' a kusa da Gidan Gwamnati
- Wasu matasa sun shiga hannun 'yan sanda a Kano bayan sun tare hanya a kusa da gidan gwamnati domin yin bidiyo a kan titi
- Kakakin 'yan sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cafke matasan da yammacin Juma’a, yana bayyana yadda suka aikata laifin
- Kiyawa ya ce an cafke su a shatale-talen gidan gwamnati yayin da suke daukar bidiyo da nufin shahara, kuma yanzu suna hannun hukuma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sabon salo na tare manyan hanyoyi a birnin Kano ya dade yana damun al'umma duba yadda ake shiga hakkinsu na yau da kullum.
Rundunar yan sanda a Kano ta sanar da cafke wasu matasa tare da yaransu kusa da gidan gwamnatin jihar yayin daukar wani bidiyo da suke yi.

Asali: Facebook
Kakakin rundunar a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yammacin yau Juma'a 23 ga watan Mayun 2025 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ke damun al'umma a Kano
Lamarin dai ya zama ruwan dare a birnin Kano yayin da matasa ke tare hanyar da al'umma ke wucewa domin gudanar da lamuransu.
Mafi yawan matasan na yin haka ne domin neman daukaka da aka fi sani da 'trending' a turance domin yaɗawa a kafofin sadarwa da suka hada da Facebook da TikTok.
Sai dai al'umma da hukumomi sun sha yin korafi kan haka inda ake kiran jami'an tsaro su ɗauki mataki kan irin wadannan matasa kafin abun ya wuce gona da iri.
Kano: Rundunar 'yan sanda ta yi gargadi
A baya, shi kansa kakakin rundunar yan sanda a jihar Kano ya sha yin gargadi kan haka inda ya tabbatar da cewa za su dauki mataki mai tsauri.
A lokacin, rundunar na magana ne bayan wasu matasa sun dauko salo inda suke tare hanya sai su fara wanka ko makamancin haka a kan titi.

Asali: Original
Sanarwar 'yan sanda kan cafke wasu matasa
Kiyawa ya ce matasan da wasu yara sun shiga hannu ne bayan tare hanya a kokarin yin 'trending' wanda ke jawo cunkoson ababan hawa a manyan hanyoyi.
Ya ce lamarin ya faru ne a kan hanya daidai shatale-talen gidan gwamnatin jihar da ke birnin Kano da ke ɗauke da dimbin al'umma da suke harkokinsu.
A cikin sanarwar, Kiyawa ya yi rubutu kamar haka:
"An kamo mutume 7 bayan sun tare hanya dai dai shatale-talen Gidan Gwamnatin jihar Kano, suna 'video' domin 'trending.'"
Kano: Yan sanda sun gwabza da yan ta'adda
A baya, idan ba ku manta ba, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta samu nasarar kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da ita ne daga jihar Kano har zuwa Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rundunar ta ce ta cafke wasu daga cikin masu garkuwar yayin wani samame da suka kai cikin dajin a kokarinsu na koro miyagu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng