Sojoji Sun Farmaki 'Dan Ta'adda Kachalla Murtala, Sun Ruguza Sansaninsa a Katsina

Sojoji Sun Farmaki 'Dan Ta'adda Kachalla Murtala, Sun Ruguza Sansaninsa a Katsina

  • Sojojin Najeriya sun kai farmaki kan sansanin jagoran ‘yan bindiga a Katsina, Kachalla Murtala inda suka yi artabu da masu ta’addanci
  • A yayin wannan samame, sojojin sun ceto wata mata mai shekaru 40 da aka yi garkuwa da ita tun sama da watanni biyu da suka wuce
  • Bayan sun fatattaki ‘yan bindigar, sojojin sun lalata sansanonin su, babura da sauran abubuwa domin hana komawar ‘yan ta’addan wajen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da wani sabon farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Katsina, lamarin da ya haifar da nasarori da dama a yaki da ta’addanci.

Samamen ya gudana ne a safiyar Asabar a kauyukan Machika da Dankolo da ke karamar hukumar Sabuwa, inda aka kai hari kan sansanonin jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Murtala.

Sojoji
Sojoji sun ceto mata daga sansanin Kachalla Murtala. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Rahotan da Zagazola Makama ya wallafa a X ya nuna cewa an kai farmakin ne bayan wani gagarumin shiri na leken asiri da hadin gwiwar jami’an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun farmaki Kachalla Murtala a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta mai zafi tsakanin dakarun sojin da ‘yan ta’addan kafin daga bisani suka tsere zuwa dazuka.

Babu rahoton asarar rai daga bangaren sojojin, amma an tabbatar da cewa an kashe ‘yan bindiga uku a yayin fafatawar da aka yi.

Bayan haka, sojojin sun lalata sansanonin, babura, dabbobi da sauran abubuwan more rayuwa na ‘yan ta’addan domin hana su komawa wuraren da suka gudu daga ciki.

An ceto matar da Kachalla Murtala ya sace

A yayin ci gaba da aikin tsabtace yankin, dakarun sun samu nasarar ceto wata mata ‘yar asalin kauyen Dankolo.

Rahotanni sun nuna cewa an sace matar ne kimanin kwanaki 70 da suka gabata a kan hanyar Funtua-Zariya.

Bayan sace ta a karon farko, matar ta samu damar tserewa daga wani sansanin ‘yan bindiga a Maigora sakamakon wani farmaki da aka kai a ranar 20 ga Mayu.

Sojoji
Sojoji za su cigaba da kai farmaki kan 'yan ta'adda a Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

An mika matar da aka sace ga iyalanta

Dakarun sojin Najeriya sun mika matar ga iyalanta cikin koshin lafiya, lamarin da ya sanya mutanen yankin murna.

Ceto matar da rushe sansanonin ‘yan bindiga ya kara bai wa jama’a kwarin gwiwa kan kokarin sojoji na dawo da zaman lafiya a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce dakarun na ci gaba da gudanar da farmaki a yankuna da dama don murkushe sauran gungun ‘yan ta’addan da ke addabar al’umma.

Sojoji sun kashe Boko Haram a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki kan 'yan Boko Haram a wasu yankuna na jihar Borno a Arewa maso Gabas.

Sojojin Najeriya sun yi kwanton bauna sun hallaka wasu 'yan ta'addan Boko Haram guda shida da suke kokarin satar kayan abinci a wata motar daukan kaya da ta baci.

Bayan kashe 'yan ta'adda shidan, sojojin Najeriya sun kashe wani dan Boko Haram da ya dauko kayan hada bom yana kokarin shiga dajin Sambisa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng