Ana tsakiyar Dambarwar Hamdiyya, Gwamnan Sokoto Ya Ɗauki Matakan Dakile Rashin Tsaro

Ana tsakiyar Dambarwar Hamdiyya, Gwamnan Sokoto Ya Ɗauki Matakan Dakile Rashin Tsaro

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya ce gwamnatinsa na daukar sababbin matakai domin yakar rashin tsaro a fadin jihar Sokoto baki daya
  • Ya bayyana cewa an raba motoci 140, babura 700 da karin alawus ga jami'an tsaro da kuma kafa hukumar 'Community Guard Corps'
  • Haka kuma, gwamnati na gina sansanin soja a Illela, da inganta na’urorin DSS da kokarin kaddamar da sansanin sojojin sama a Sokoto

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin tsaro a fadin jihar.

Gwamna Aliyu ya sanar da wasu sababbin matakai yayin taron majalisar zartarwa na jihar a ranar Laraba 21 ga watan Mayun 2025.

Gwamnan Sokoto ya magantu kan matsalar tsaro
Gwamnatin Sokoto ta dauki matakai kan matsalar tsaro. Hoto: @ahmedaliyuskt.
Asali: Twitter

Gwamnan Sokoto ya magantu kan matsalar tsaro

Yayin jawabinsa a fadar gwamnati, Gwamna Aliyu ya bayyana cewa an kashe biliyoyin Naira domin karfafa karfin hukumomin tsaro kamar yadda ofishin sakatarensa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa kamar yadda ya yi alkawari tun farko domin kawo karshen matsalar tsaro.

Alƙawarin gwamnatin Sokoto kan matsalar tsaro

Tun farko, a lokacin da yake kamfen domin neman kujerar gwamna a Sokoto, gwamnan ya ce ko da kudin jihar za su kare zai kashe saboda inganta tsaro.

“Muna bai wa hukumomin tsaro cikakken tallafi tare da bullo da sababbin hanyoyi don dakile ayyukan 'yan bindiga."

- Cewar gwamnan yayin taron

Daga cikin matakan da aka dauka akwai raba motoci 140 na sintiri, karin alawus ga jami’an tsaro a wuraren daban-daban da kuma kafa hukumar 'Community Guard Corps' a Sokoto.

Ya bayyana cewa an bai wa wannan runduna sababbin motoci kirar Hilux guda 40 da babura 700 domin inganta motsi da karfin aiki na jami’an rundunar.

Gwamnatin Sokoto ta sha alwashi kan tsaro
Sababbin dabarun gwamnatin Sokoto kan matsalar tsaro. Hoto: Office of the Press Secretary, Government House Sokoto.
Asali: Facebook

Tsaro: Matakan da gwamnan Sokoto ke dauka

Gwamna Aliyu ya kuma bayyana wasu karin matakai kamar inganta tsarin gano bayanan DSS zuwa fasahar 5G da samar da babura ga jami’an na DSS.

An kuma kafa hedkwatar hukumar 'Community Guard Corps' a matakin kananan hukumomi da na jiha tare da gina sansanin soja a karamar hukumar Illela.

Ya kara da cewa ana ci gaba da kokari domin ganin an kaddamar da sansanin sojojin sama a jihar Sokoto.

Bukatar gwamnan Sokoto ga majalisar zartarwa

Gwamnan ya bukaci mambobin majalisar zartarwa da su kara zage damtse domin tallafa wa shirye-shiryen gwamnati wajen tabbatar da tsaro da ci gaba.

Aliyu ya gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayansu da addu’o’insu, tare da bukatar hadin kai wajen yaki da rashin tsaro.

An gano Hamdiyya bayan ɓacewarta a Sokoto

Kun ji cewa rahotanni sun ce an gano Hamdiyya Sidi Shareef a babban asibitin Bakura da ke Zamfara cikin mawuyacin hali.

Lauyanta, Abba Hikima, ya ce an sace ta ne a Sokoto lokacin da ta fita sayo kayan miya, kuma yanzu haka jami'an tsaro na tare da ita.

Hakan ya biyo bayan ɓacewarta a ranar Talata bayan ta fita sayan kayan abinci lamarin da ya tayar da kura musamman a kafofin sadarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.