Sule Lamido Ya Faɗi Karon Battarsa da Jonathan a 2015 da Gargaɗin da Ya Yi Masa

Sule Lamido Ya Faɗi Karon Battarsa da Jonathan a 2015 da Gargaɗin da Ya Yi Masa

  • Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da kullawa dansa makirci
  • Ya fadi yadda aka kama dansa a 2014 da $50,000 yayin da yake hanyar kai ‘yarsa jinya, amma gwamnati ta buga labarin da sunan cin hanci
  • A cikin littafinsa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana yadda ya fuskanci Jonathan, ya fada masa shi bafillace ne kuma zai rama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan karon battarsa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Sule Lamido ya bayyana cewa ya taba gargadin Goodluck Jonathan kan wahalar da ya jefa iyalinsa a ciki.

Lamido ya magantu kan rigimarsa da Jonathan
Lamido ya koka kan abin da Jonathan ya yi masa. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Facebook

Sule Lamido ya fadi silar matsalarsa da Jonathan

A littafinsa “Being True to Myself” da aka fitar a 13 ga Mayu, Sule Lamido ya ce an kama dansa a Kano yana tare da ‘yarsa da za a kai jinya a Cairo, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule ya ce matsalolinsa da gwamnatin Jonathan sun fara ne a 2014, bayan Olusegun Obasanjo ya karfafa masa gwiwa ya tsaya takarar shugaban kasa.

Ya bayyana kama dansa a matsayin wani yunkuri daga gwamnatin Jonathan don kai farmaki a kansa da iyalinsa.

Ya ce:

“An kama shi ne a tafiyar su ta uku, yana dauke da $50,000. Yana tare da matarsa, ‘yarsa mai jinya da kuma mai kula da ita. Kudin na jinya ne.

Sule ya ce manufar hakan ita ce a bata masa suna da kuma dakile karfinsa inda ya ce ya gana da Jonathan ya bayyana fushinsa, tare da gargadi mai tsanani.

A cewarsa:

“Mu duka muna jam’iyyar PDP ce, wanda ka samu cigaba cikinta daga NDDC har zuwa zama Shugaban Najeriya.
“Ta yaya za ka yi amfani da karfin mulkinka domin azabtar da ni saboda kawai wani ya fada maka ina da burin shugabanci?”
“Shugaba, ka yi tunani, shin $50,000 na iya lalata tattalin arzikin Najeriya?”

“Ni tsohon Ministan Harkokin Waje ne, kuma na san da batun badakalar man Malabu da ta kai dala biliyan 1.2.”
Gargadin da Sule Lamido ya yi ga Jonathan
Sule Lamido ya zargi Jonathan da bata masa suna. Hoto: Sule Lamido, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Gargadin Sule Lamido ga Goodluck Jonathan

Lamido ya ce ba wai yana barazana ga Jonathan ba ne, sai dai yana son bayyana gaskiya game da abin da ya faru.

Ya ce ya fada wa Jonathan cewa a matsayinsa na Bafillace, zai rama azabar da aka jefa shi da iyalinsa.

A cewarsa:

“Shugaba, na ji ciwo matuka saboda kana kokarin bata sunana da na iyalina. Ba fushi nake ba, amma zan rama.
“Ni Bafillace ne, ba ma mantuwa, wata rana zan dauki fansa kan azabar da ka jefa mu a ciki.”

Sule Lamido ya ce kalamansa sun girgiza Jonathan, wanda ya amsa da cewa, 'Jigawa, zan yafe wa danka'.

Na ce masa cikin mamaki:

“Ashe da gaske ne? Ka na tabbatar mani cewa lamarin shiri ne tun farko?
“An riga an yanke masa hukunci da tara. Mun daukaka kara, daga nan zuwa kotun koli, sai kai ka yafe masa. Ashe shiri ne tun farko?”

“Yanzu na fahimta. Ka sani, za ka dandana kudarka kan hakan.”

'Dan siyasar a ce ya bar fadar Shugaban kasa cikin bacin rai, yayin da Jonathan ya yi shiru, ya kasance cikin tunani.

Sule Lamido ya fadi yadda Abacha ya kama shi

Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan yadda ta kaya tsakaninsa da marigayi Janar Sani Abacha.

Tsohon gwamnan ya ce Abacha ya sha alwashin mika mulki ga farar hula, amma daga baya ya fasa, wanda hakan ya janyo sabani tsakaninsu.

Lamido ya ce kin yarda da tsarin mulkin Abacha ya sa aka cafke shi da Abubakar Rimi a wancan lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.