Zaben 1993: Sule Lamido Ya Faddi Yadda Ta Kaya tsakaninsa da IBB kan Soke Nasarar Abiola
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana yadda ya cire tsoro yayin tattaunawarsu da Janar Ibrahim Badamasi Babangida
- Sule Lamido ya bayyana cewa ya kalli idon IBB ya gaya masa cewa ya yi murabus kan soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993
- Babban 'dan siyasar ya nuna cewa IBB ya yi mamakin yadda ya yi tsaurin ido har ya iya gaya masa ya yi murabus lokacin yana ganiyar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan tattaunawar da suka yi da tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Babangida, kan zaɓen ranar 12, ga watan Yunin 1993.
Sule Lamido ya bayyana cewa ya roƙi Babangida da ya yi murabus bayan soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 1993 da MKO Abiola ya lashe a ranar 12 ga watan Yuni.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce hakan na cikin wani ɓangare na littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna “Being True to Myself” da aka ƙaddamar a ranar 13 ga Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IBB ya yi wa Sule Lamido martani mai zafi
Sule Lamido wanda shi ne sakataren jam'iyyar SDP na ƙasa da aka rushe, ya tuna da martanin Babangida wanda ya ce babu wani ɗan Najeriya da zai iya kallon fuskarsa ya gaya masa ya yi murabus.
A babi na bakwai na littafin da aka sanya wa suna "June 12 Consumes IBB", Lamido ya rubuta cewa:
"Ina zaune a ɗakin otel na Nicon Noga Hilton (wanda yanzu ake kira Transcorp Hilton) da safe, sai wayata ta yi ƙara. Muryar da ta kira ta gabatar da kanta da sunan Kanal Bamalli, ya ce C-in-C (shugaban ƙasa) yana so ya gan ni yanzu."
"Saboda ban saba da tsarin ba, sai na tambaya waye C-in-C? Sai Bamalli ya ce: "Shugaban ƙasa." Sai na ce amma fa yanzu na farka, ko wanka ban yi ba."
"Ban sani ba a she Babangida yana kan ɗayan layin, sai na ji muryarsa ya ce: 'Kai Sule, ka zo yanzu!’ Na ce, ‘To, ranka ya daɗe!’"
Sule Lamido bai gamsu da bayanin IBB ba
Sule Lamido ya bayyana cewa bai gamsu da hujjojin Babangida na soke zaɓen ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da zancen.
A lokacin ganawarsu a fadar shugaban ƙasa, Babangida ya ce Abiola ba zai iya zama shugaban ƙasa ba saboda yana bin gwamnati bashi.
Ya ce a ganawarsu, wacce ita ce karo na farko da suka haɗu, Babangida ya fahimci cewa yana da gaskiya da ƙwarewar aiki.

Asali: Twitter
“A matsayina na sakataren SDP na ƙasa, na shaida masa cewa mun gama duk wata muhawara da gwamnatin soja game da zaɓen 12 ga Yuni. Babu wani sabon zaɓe da za mu shiga. A wajenmu, sai dai zaɓen 12 ga Yuni ko a bar shi kawai."
“Sai Babangida ya tambaye ni, ‘Sule, me kake ganin ya kamata na yi?’ A cikin gaskiya da rashin wata manufa, na ce masa kai tsaye, ‘Ranka ya daɗe, dole ne ka yi murabus, ka bar ofis.’”
“Da na faɗi haka, sai fuskarsa ta canza gaba ɗaya. Na ga wuta a idanunsa, na ɗan lokaci bai iya cewa uffan ba.”
"Sai Babangida ya kalle ni ya ce 'Sule, babu wani ɗan Najeriya da zai iya ce min haka, kuma na san ƴan Najeriya sosai. Ban taɓa tunanin kai ka isa ka ce haka ba. Ka yi sa’a. Ina ganin kana da tsoron Allah.”
- Sule Lamido
Sule Lamido ya yi fallasa kan Abba Kyari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa marigayi Abba Kyari ya taɓa yi musu tayin cin hanci.
Sule Lamido ya bayyana cewa marigayin ya ba su cin hancin N160m da shi da Abubakar Rimi domin su taimaka masa ya zama mataimin Olusegun Obasanjo.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Abba Kyari ya bar wajen cike da kunya bayan sun ƙi karɓar tayin da ya yi musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng