Gwamna Abba Ya Shiga Tarihi, Ya Amince a Kafa Sabuwar Kwalejin Fasaha a Kano

Gwamna Abba Ya Shiga Tarihi, Ya Amince a Kafa Sabuwar Kwalejin Fasaha a Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha a Gaya, don fadada damar ilimi da koyon sana’o’i a Kano
  • Gwamnati ta kafa kwamitin da zai tsara gina sabuwar kwalejin; wannan zai sa Kano ta mallaki jami’o’i biyu da kwalejoji biyu na jiha
  • Matakin ya yi daidai da manufofin Gwamna Abba na inganta ilimi, inda ya riga ya dauki matakai da dama, ciki har da fitar da dalibai waje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha ta jiha a karamar hukumar Gaya.

Wannan mataki yana daga cikin kudirin gwamnatin Abba na farfado da ilimi da kuma fadada damar samun horon fasaha ga matasa a fadin jihar.

Gwamna Abba Yusuf ya amince da kafa sabuwar kwalejin fasa a Kano
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Gwamna Abba zai kafa kwalejin fasaha a Kano

Mai tallafawa Gwamna Abba kan kafofin sadarwa na zamani, Abdullahi I. Ibrahim, ya sanar da wannan ci gaba a ranar Talata, 20 ga watan Mayu, 2025, a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar Abdullahi, an kafa wani kwamiti na mutum 15 da zai tsara yadda za a aiwatar da gina wannan sabuwar makaranta da za ta dinga ba da horo na sana'o'i da fasaha.

Da zarar an kammala kafa kwalejin Gaya, Kano za ta mallaki jami’o’in jiha guda biyu da kuma kwalejojin fasaha biyu, wanda hakan zai kara wa jihar armashi a fannin ilimi.

Sanarwar Abdullahi ta bayyana cewa:

"Gwamna Abba K. Yusuf ya amince da kafa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha ta jiha a karamar hukumar Gaya.
"Da zarar an kammala kafa ta, jihar Kano za ta mallaki jami’o’in jiha biyu da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na jiha biyu."

Gwamna Abba na sauke alkawarin da ya dauka

Kodayake ba a bayyana cikakken tsarin karatu da kasafin kudin gina makarantar ba, kafa kwamitin da zai jagoranci aikin ya nuna cewa shirin aikin yana a matakin farko.

Wannan shiri ya yi daidai da wasu matakan da Gwamna Abba ya dauka a baya, ciki har daukar dalibai 54 aiki bayan sun kammala karatu a kasashen waje.

Wasu daga cikin bayanan da suka fito na nuna cewa kafuwar kwalejin Gaya na cikin alkawuran da gwamnan ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.

Gwamnan jihar Kano ya kafa kwamitin da zai taimaka wajen kafa sabuwar kwalejin fasaha a Gaya
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Sunayen 'yan kwamitin kafa sabuwar kwalejin Kano

Harilayau, a shafinsa na X, Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa wata takarda wadda ke dauke da sunayen mutum 15 da ke cikin kwamitin tsara yadda za a kafa kwalejin.

Legit Hausa ta zakulo sunayen 'yan kwamitin da suka hada da:

  1. Dr. Hadi Bala Yahaya mni – Shugaba
  2. Dr. Muhammad Umar Kibiya – Shugaba na biyu
  3. Prof. Auwalu Halilu Arzai – Mamba
  4. Alhaji Ibrahim Jibrin Fagge – Mamba
  5. Engr. Yahaya Abubakar Baba – Mamba
  6. Prof. Abba Garba Gaya – Mamba
  7. Dr. Garba Adamu – Mamba
  8. Arch. Aminu Muhammad Abdullahi – Mamba
  9. Wakilin ma'aikatar shari'a – Mamba
  10. Wakilin ma'aikatar kudi – Mamba
  11. Dr. Surajo Isa Gaya – Mamba
  12. Mal. Sa’idu Sulaiman – Mamba
  13. Usaini Ali Ajingi – Mamba
  14. Shehu Sani Shehu – Mamba/Sakatare
  15. Dr. Lukman T. Siraj – Mamba/Mataimakin sakatare

Alkawarin da Abba ya dauka kan ilimi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf ya sha alwashin gyara tsofaffin makarantu da gina sababbi domin inga ilimi a jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wata ziyarar ba zata a kwalejin kimiyya da fasaha ta mata da ke kofar Nassarawa a jihar, a watan Yuli, 2024.

Abba Yusuf ya ce bai ji dadin halin da makarantun jihar da sauran bangarorin sashen ilimi ke ciki ba a lokacin suka karbi mulki, amma ya sha alwashin gyara komai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.