Dalibi Musulmi Ya Doke Takwarorinsa Kiristoci, Ya Lashe Gasar 'Bible' da Aka Gudanar
- Wani yaro Musulmi mai shekaru 9, Muritala Desmond, ya lashe gasar Littafi Mai Tsarki ta makarantu da Bible Society of Nigeria ta shirya a Lagos
- Desmond, ɗalibi a Salem Baptist International School, ya ci maki 100% duk da rashin goyon bayan kakarsa da bambancin addininsa
- Hukumar BSN ta bukaci goyon bayan jama’a don ci gaba da shirya irin waɗannan gasa da kuma bai wa yara tallafi da kyaututtuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Wani dalibi Musulmi a jihar Lagos ya yi bajinta a cikin dalibai takwarorinsa Kiristoci.
Dalibin ya yi fice a gasar karatun Littafi Mai Tsarki ta yara karo na hudu da Bible Society of Nigeria ta shirya.

Asali: Facebook
Yadda Musulmi ya lashe gasar Kiristoci a Lagos
A gasar da aka gudanar a Salvation Army, Onipanu, Muritala Desmond, ɗalibi Musulmi mai shekaru 9 daga Salem Baptist School, ya lashe gaba ɗaya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Desmond, wanda ke aji 4, ya ci maki 100%, ya doke Phoebe Fashola da Success Olawoyin na Grand Royale da suka samu 90%, da Anabel Ogechi da ta ci 85%.
Gasar, wacce aka shirya karo na hudu, ta haɗa makarantu 17 daga Legas, inda 6 suka samu zuwa zagaye na ƙarshe na gwajin sanin Littafi Mai Tsarki.
Duk da bambancin addini da kin amincewar kakarsa a farko, Desmond ya ce:
“Ina son Littafi Mai Tsarki saboda darussan ɗabi’a da ke cikinsa, ina karatu na tsawon awa ɗaya kullum cikin mako tare da malamai, wannan ya taimaka wajen samun nasarar da muka cimma yau.”
Malamar Desmond, Barwa Adeyemi, ta ce:
“Yaron yana da wayo, ladabi kuma ya rasa mahaifiyarsa tun yana ƙarami, yana da kyakkyawan hali sosai.”
Grace Benjamin, mai kula da shirye-shirye a BSN, ta ce:
“Muna ƙoƙari mu dawo da kyawawan halaye ga yara domin su guji munanan dabi’u.”
“Idan muka soma da yara tun suna ƙanana, za su girma da kyawawan halaye da za su gina al’umma ta gari da tsoron Allah.”

Asali: Original
Yadda ake gayyatar dalibai a gasar
Benjamin ta bayyana cewa sun gayyaci makarantu da dalibai ta hanyar sada zumunta da saƙonnin kai tsaye. Yara sun amsa tambayoyi daga littafin 'My 100 Best-Loved Bible Stories'.
“Bayan gasar, yara sun yi mu’amala da juna da karatu wajen da ba makaranta ba. Wannan yana taimaka musu fiye da karatu kawai.:
“Muna so mu raina yara da suka kware a fannin addini kamar yadda ake raina waɗanda ke kwarewa a fannin ilimin boko.”
BSN ta raba jakunkunan makaranta, Littattafan Injila, kayan karatu kamar Scrabble, lambar yabo da kyaututtuka ga makarantu masu nasara, cewar The Nation.
Daliba ta lashe gasar 'Spelling Bee' a Lagos
Kun ji cewa an bayyana cewa Jemimah Marcus wacce ta yi nasara a gasar Spelling Bee da aka gudanar a Lagos.
Dalilin hadakar da ta yi dalibar ta ci kyautar 'gwamnan kwana guda' wanda ta yi galaba kan sauran ‘yan makaranta a fadin jihar.
Dalibar ta tashi da kyaututtuka masu dinbin yawa ciki har da kyautar kudi N250, 000 da aka ba ta a dakin taro na Adeyemi Bero, Alausa, garin Ikeja.
Asali: Legit.ng