Jemimah Marcus ta lashe gasar Spelling Bee, za ta zama ‘Gwamna’, ta ci N250, 000
-A gasar Spelling Bee na shekarar bana, Jemimah Marcus ce ta yi nasara
-Marcus za ta zama Gwamnan kwana daya, kuma ta samu kudi N250, 000
-Gwamnati za ta dauki nauyin duk karatun wannan Baiwar Allah a Jami’a
Jemimah Marcus, wata daliba a makarantar Angus Memorial Senior High School da ke garin Legas, za ta zama gwamnan Legas na kwana daya.
Punch ta bayyana cewa Jemimah Marcus tayi nasara a gasar Spelling Bee da aka gudanar jiya, don haka ta ci kyautar 'gwamnan kwana guda'
Wannan babbar galaba da Miss Jemimah Marcus ta yi a kan sauran ‘yan makaranta a fadin jihar, ya sa ta tashi da kyaututtuka masu dinbin yawa.
Daga cikin kyautar da wannan hazikar daliba ta samu akwai kudi har N250, 000 da aka ba ta a dakin taro na Adeyemi Bero, Alausa, garin Ikeja.
KU KARANTA: COVID-19: Gwamnan Legas ya killace kansa
Wanda ya zo na biyu a wannan gasa shi ne Ajose Sotin na makarantar Topo Senior Grammar School, Badagry, shi kuma ya tashi da N150, 000.
Rhema Edeh daga makarantar Denton Junior Grammar, Ebute-Metta ya samu kyautar N100, 000.
Kwamishinar ilmi ta jihar Legas, Folasade Adefisayo, ta halarci wannan gasa, ta kuma yi kira ga wadanda su ka yi nasarar, su kara kokari a makaranta.
Ta ce: “Kamar yadda aka saba, gwamnatin Legas za ta dauki dawainiyar gwamnan kwana dayan, ya zabi jami’ar da yake so cikin kasar nan ya yi karatu.”
KU KARANTA: Gwamna ya fadi wadanda su ka yi harbi a kofar Lekki
Adefisayo ta yabawa Sanata Oluremi Tinubu da ta kirkiro wannan shirin da ke taimakawa yara.
A makon jiya kun ji cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kamu da Coronavirus.
An tabbatar da cewa cutar ta harbi gwamnan ne a ranarAsabar, 12 ga watan Disamba, 2020. Daya daga cikin hadimansa, Jubrin Gawat, ya bayyana haka.
Daga baya, kwamishanan harkar kiwon lafiya na Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya fitar da jawabi game da lamari. Tuni dai gwamnan ya killace kansa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng