Ana Jimamin Abin da Ya Faru a Neja, Guguwa Mai Karfi Ta Kifar da Jirgi a Najeriya

Ana Jimamin Abin da Ya Faru a Neja, Guguwa Mai Karfi Ta Kifar da Jirgi a Najeriya

  • Wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 22 da ya taso daga Fatakwal zuwa Bonny ya nutse, mutum sun rasa rayukansu
  • Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a kusa da yankin da ake kira ‘Yellow Platform,’ sakamakon wata iska mai ƙarfi
  • Rundunar ƴan sanda reshen Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an yi nasarar ceto mutum 19 amma uku sun riga mu gidan gaskiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Wani mummunan hatsari ya rutsa da jirgin ruwan da ya taso daga Fatakwal zuwa Bonny a jihar Ribas ranar Lahadi.

Hatsarin jirgin ruwan ya yi sanadiyyar rasa rayuka uku daga cikin fasinjoji 22 da lamarin ya rutsa da su.

Taswirar jihar Rivers.
Hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukan mutum 3 a jihar Ribas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a wani yanki da ake kira ‘Yellow Platform,’ kusa da tsibirin Bonny.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Guguwa mai ƙarfi ta kifar da jirgin ruwa

Bayanai sun nuna cewa jirgin ya yi tangal-tangal sakamakon wata guguwa mai ƙarfi da ta tashi ba zato ba tsammani, daga bisani kuma ya nutse a ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan ya tashi daga tashar Bonny/Nembe/Bille da ke Fatakwal, yana ɗauke da fasinjoji 22.

An yi nasarar ceto mutum 19 daga cikin fasinjojin da ransu, yayin da sauran uku, maza biyu da wata ƙaramar yarinya suka rasa rayukansu a wannan mummunan al’amari.

Ƴan sanda sun tabbatar da faruwar hatsarin

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin abin tausayi da takaici.

Ta ce:

“Abin bakin ciki ne ƙwarai, amma an ceto mutane 19 da ransu. Jirgin ya kife a kusa da yankin Yellow Platform a Bonny yayin da yake kan hanyarsa daga birnin Fatakwal.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya haifar da hatsarin.”

Abin da ya jawo kifewar jirgin ruwa

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta reshen jihar Ribas, Israel Pepple, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon guguwar iska mai ƙarfi.

Ya ƙara da cewa irin wannan guguwa kan zama barazana ga jiragen ruwa, musamman idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

Haka zalika, shugaban ƙaramar hukumar Bonny, Anengi Claude-Wilcox, ya nuna alhininsa kan wannan mummunan al’amari, Punch ta kawo.

A cewarsa, “Wannan babban rashi ne ga al’ummarmu. Muna taya iyalan waɗanda suka rasa rayukansu juyayi, kuma muna fata cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”

Mutane sun nuna damuwa kan haɗurran jirgi

Hatsarin ya jawo damuwa kan tsaron jiragen ruwa a yankin, tare da jaddada bukatar ɗaukar tsauraran matakai don kare rayukan fasinjoji.

Mutanen da ke amfani da jiragen ruwa sun yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da bin dokokin tafiyar ruwa don gujewa irin wannan mummunan lamari nan gaba.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a bikin nadin sarauta, ana fargabar an sumar da jami'ar NSCDC

Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa mutum ɗaya ya rasu a hatsarin jirgin ruwan da =a rutsa da fasinjoji sama da 30 a jihar Sakkwato.

Gwamnatin jihar Sakkwato ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce masu aikin ceto sun yi nasarar ceto fasinjoji 34 da ransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262