Gwamnan PDP Ya Fadi Yadda Ya Biya Bokaye N5m domin Samun Kujerar Gwamna
- Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana yadda ya biya matsafa a Kenya $10,000 don kokarin ba shi nasarar zama gwamna ta
- Sanata Diri ya bayyana yadda babban mutum ya bukace shi ya yi wani hadaya a Abuja, amma ya ki saboda yakininsa da Ubangiji
- Gwamnan ya jaddada bukatar siyasa ta dogaro ga Ubangiji, yana mai cewa Allah ne ya tabbatar da nasararsa duk da kalubale
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Yenagoa, Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yi magana kan neman takarar siyasarsa.
Gwamna Diri ya bayyana yadda ya biya wasu yan tsibbu a Kenya $10,000 kimanin N5m domin kokarin taimaka masa ya zama gwamna.

Asali: Twitter
Yadda gwamna ya biya bokaye kan kujerar siyasa
Diri ya fadi haka ne yayin bikin ranar gode wa Ubangiji ta shekara-shekara da aka gudanar a Sampou, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka, Diri ya ce ya ki amincewa da yin wani hadaya da aka bukata domin samun kujerar gwamna.
Ya ce tsabar amincewarsa da dogaro Ubangiji ta sa aka yi masa lakabi da "Gwamna mai mu'ujiza".
Ya kara da cewa a shekarar 2020, wani babban mutum ya gayyace shi zuwa Abuja ya bukaci ya yi sadaukarwa idan yana son zama gwamna, amma ya ki amincewa, The Nation ta ruwaito.
Sanata Diri, wanda ya tsaya takarar gwamna a 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, ya sha kaye a wajen dan takarar APC, Cif David Lyon.
Sai dai, ya kalubalanci sakamakon zaben da INEC ta bayar har zuwa Kotun Koli, inda ya samu nasara.
Mai magana da yawun gwamna, Daniel Alabrah, ya bayyana cewa wani babban mutum ya kawo yan tsubbu daga Kenya domin yin hadaya yayin da shari’ar ke Kotun Koli, amma gwamnan ya ki amincewa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Diri ya ce mutumin ya bukaci kudin da aka kashe don kawo bokayen, inda ya biya $10,000 domin biyan bashin.
Gwamna ya shawarci yan siyasa a lamuransu
Ya jaddada cewa dogaro da ya yi da Ubangiji ne ya hana shi neman taimako daga wani wuri inda ya bukaci 'yan siyasa su dauki darasi, su dogara da Ubangiji ba mutane ba, domin shi ne mai iya dukkan al’amura.
Ya nuna godiya ga Rabaran David Zilly Aggrey da wadanda suka ci gaba da gudanar da wannan shiri, yana mai cewa addu’arsu ta sa Ubangiji ya tabbatar da nasararsa.
A yayin kin wa’azinsa, Fasto Aggrey ya ce matasa ba za su gane muhimmancin wannan godiya ba saboda ba su san irin wahalhalun da dattawa suka sha ba.
Gwamna Diri ya yaba wa tasirin siyasar Jonathan
Kun ji cewa Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya bayyana yadda tafiyar siyasarsa ta kasance ƙarƙashin Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan
'Ni kadai ke da iko': Gwamnan APC ya rikita zaman makoki, ya gargadi maciya amana
Gwamnan ya ce tsarin tsohon shugaban ya taba masa siyasa kafin ya zama ɗan Majalisar Tarayya a shekarar 2015.
Diri ya fadi irin tasirin da matakin Jonathan ya yi a siyasarsa a jihar Bayelsa da yadda hakan ya zamo masa alheri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng