Tinubu Ya Dauki Matakin Farfaɗo da Arewa Maso Gabas, Kashim Shettima Ya Yi Karin Haske

Tinubu Ya Dauki Matakin Farfaɗo da Arewa Maso Gabas, Kashim Shettima Ya Yi Karin Haske

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka kan Arewa maso gabas
  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka ne yayin kafa tubalin hedikwatar hukumar raya yankin Arewa maso gabas a jihar Borno
  • Shugaban gwamnonin yankin kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira ga shugabannin Arewa maso gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya kafa tubalin hedikwatar hukumar raya Arewa maso gabas (NEDC) a jihar Borno.

Mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar shugaban gwamnonin Arewa maso gabas kuma gwamnan Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya yayin bikin.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Hukumar NEDC
An kafa tubalin hedikwatar hukumar NEDC a Borno. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani sako da mai taimakawa gwamnan jihar Gombe a harkokin sadarwa, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin Tinubu a Arewa maso gabas

Yayin kafa tubalin hedikwatar, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa aikin na daya daga abubuwan da shugaban kasa Bola Tinubu yake yi domin haɓaka tattalin arzikin Arewa maso gabas.

Ya ce aikin har yanzu na nuna Bola Tinubu yana kokari wajen cika alkawuran da ya yiwa Arewa maso gabas domin ganin yankin ya cigaba.

Haɗin kai a Arewa maso gabas

Mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa akwai bukatar kara samun haɗin kai a yankin Arewa maso gabas.

Shettima ya tabbatar da cewa da hadin kai ne kawai za a iya dawo da martabar yankin wanda ayyukan yan ta'adda ya kawowa koma baya.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Boko Haram ta sa aka kafa hukumar NEDC

Shugaban gwamnonin yankin Arewa maso gabas, Alhaji Inuwa Yahaya ya ce ayyukan ta'addanci sun mayar da yankin baya da kimanin shekaru 50.

Saboda haka ya yi kira ga shugabannin yankin da masu ruwa da tsaki wajen taimakawa da kula da ayyukan NEDC domin ganin an cimma burin farfaɗo da yankin.

Hukumar NEDC za ta gina makarantu

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar raya yankin Arewa maso gabas (NEDC) ta bayyana kudurin gina makarantu a jihohin da ta ke aiki.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta bayyana dalilin gina makarantun da cewa, hakan zai habaka ilimi a yankunan da Boko Haram ta lalata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng