'Talauci ne': Ministan Buhari Ya Fadi Dalilin Shiga Siyasa, Ya Bugi Kirji kan Kafa APC
- Tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin tarayya, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin fadawarsa cikin siyasa ba ji ba gani
- Rt. Hon. Amaechi ya bayyana cewa talauci ne ya sa ya tsaya tsayin daka a siyasa tun bayan kammala jami'a a shekarar 1987
- Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa ‘yan siyasa a Najeriya suna amfani da mukamansu ne don sata, cin zarafi, da kuma riƙe mulki ta kowace hanya
- Ya ce ba za a iya shafe rawarsa a kafa jam’iyyar APC ba, kuma a dalilin tsayuwar daka, PDP da Goodluck Jonathan sun mika mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa talauci da buƙata ne suka tilasta masa kasancewa cikin siyasa tun bayan kammala jami’a a 1987.
Tsohon gwamnan Rivers ya fayyace irin muhimmiyar rawar da ya taka yayin kafa jam'iyyar APC a Najeriya inda ya ce babu wanda zai raina tasirinsa a siyasa.

Asali: Facebook
Rotimi Amaechi ya yi alfahari da kafa APC
Amaechi ya bayyana hakan ne a bidiyo da Punch ta wallafa yayin taron ƙasa kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya da aka gudanar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya ƙara da cewa kasancewarsa a siyasa, musamman jam’iyyar APC, ya sa ba za a iya shafe rawarsa ba cikin harkokin siyasa a Najeriya.
Ya koka da halayen yan siyasa musamman a lokutan zaɓe inda suke yaudarar mutane da kudi.
Musabbabin shigan Amaechi siyasa bayan gama jami'a
“Abin takaici, talauci ne ya sa na kasance a siyasa tun bayan barin jami’a a 1987, kuma har yanzu ina cikin tsarin.
“Ba za ku iya shafe rawar da na taka a kafa jam’iyyar APC ba, kuma ba za ku iya shafe rawata a yadda ta ci zaɓe ba, ba zai yiwu ba."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya tona asirin APC a Jonathan
Kun ji cewa tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana yadda suka biya mata don yin zanga-zanga a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Tsohon gwamnan Rivers ya ce ya sha mamaki a lokacin da ya je wurin taron domin gane wa idonsa yadda shirin ke tafiya inda suka yaudare su.
Amaechi ya caccaki masu jefa kuri'a a Najeriya, yana cewa yawancinsu suna bin 'yan siyasa ne saboda kyauta da alkawarin kudi da suke yi a lokutan zaɓe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng