Akpabio: Asiri Ya Tonu kan Yadda aka 'Kullawa' Sanata Natasha Sabon Makirci
- Fitacciyar 'yar jarida, Francess Ogbonnaya ta zargi Farfesa Sandra Duru da neman hadin kanta domin bata sunan Natasha Akpoti-Uduaghan
- Ta bayyana cewa an biya ta N300,000 domin ta hada sautin muryar da ya zargi Sanata Natasha da wasu maganganu da za su ta da kura
- Ogobonnaya ta kara da cewa daga cikin abubuwan da aka ce ta hada har da cewa Sanatar ta Kogi ta na son kifar da gwamnatin Yarbawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shahararriyar mai aiki a kafar yada labaran, Francess Olisa Ogbonnaya, ta zargi Farfesa Sandra Duru da ba ta kuɗi domin ta shirya muryar bogi da nufin bata sunan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Ogbonnaya, ta zargi Farfesa Sandra Duru da bata N300,000 domin ta ƙirƙiri sautin muryar da aka shirya da nufin bata sunan Sanatar Kogi da aka dakatar daga majalisa.

Asali: Facebook
Leadership a ruwaito a cewar Ogbonnaya, daga cikin abubuwan da ke cikin wannan rubutaccen shiri har da wani zargin cewa wai Sanata Natasha tana so ta “kifar da gwamnatin Yarbawa.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba Natasha kariya a zargin kifar da gwamnati
Daily Post ta ce Farfesa Sandra Duru ta tura mata rubutaccen saƙo inda ta bukace ta ta karanta sakon da muryarta, amma Ogbonnaya ta ƙi saka sassan da take ganin sharri ne.
Obonnnaya ta ce:
“Ta ya kuke tunanin cewa Sanata Natasha za ta kifar da gwamnatin Yarbawa?” “Mutanen Kogi ba su da rinjaye a Najeriya.Wani lokacin ma suna kusantar Yarbawa. Wasu lokutan ma ana ɗaukar Igala a matsayin Ibo.”

Asali: Facebook
Ogbonnaya ta ƙara da cewa Duru ta fusata bayan ta fitar da 'ƙaryar' daga cikin sautin da aka shirya, sai ta bukaci a maido mata da kuɗinta.
“Da na cire ƙaryar daga ciki, sai ta fara fushi da cewa wai ina hana ta cimma shirin ta.”
Yadda aka kitsawa Natasha Akpoti ‘karya’
Wannan takaddama ta biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka ji Farfesa Sandra Duru na cewa wai Sanata Natasha ta yi karairayi da yawa.
Ta ce Natasha ta amsa cewa ta ƙirƙiro zargin cin zarafin da ta ke yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Domin tabbatar da maganganunta, Ogbonnaya ta gabatar da hotunan tattaunawa ta WhatsApp, rasitin biyan kuɗi da sauran bayanai.
Natasha ta ce ana kokarin kama ta
A baya, mun wallafa cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce tana cikin fargaba domin ta samu labarin cewa jami’an tsaron Najeriya na shirin cafke ta da zarar ta dawo daga Amurka.
Ta bayyana cewa tana ganin wannan shiri na cafke ta yana da nasaba da taron IPU da ta halarta, duk da cewa wasu na ganin ba ta samu sahalewar gwamnati ko majalisa ba ta je.
Rahotanni sun bayyana cewa ba ta fadi sunan wata hukuma kai tsaye da ke da alhakin wannan shirin kama ta ba, sai dai hakan na ƙara tayar da kura a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng