“Ba Rikici Tsakanina da Kawu Sumaila,” Sanata Sani Musa ya Kunyata Magauta
- Sanata ya bayyana cewa, bai kamata a yi kokarin hada shi da fada da dan uwansa sanata a majalisar dattawa ba
- Sanata Sani Musa ya ce akwai alaka mai karfi tsakaninsa da Sanata Kawu Sumaila, a daina yada jita-jita
- An yada labarin jita-jita da ke nuni da yadda sanatan ya yi martani kan tsokacin sanata Sumaila a majalisa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abuja – Sanata Mohammed Sani Musa, dan majalisar dattijai daga jihar Neja, ya fito fili ya karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke danganta shi da sabani da Sanata Kawu Sumaila dangane da kasafin kudin shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Sanata Sani Musa ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma an fitar da shi ne domin tayar da kura da haddasa rikici tsakaninsa da abokin aikinsa, Sanata Sumaila, wanda kwanan nan ya koma jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Sanatan ya bayyana cewa a shekarar 2023 ya mayar da martani ne kan wani rubutu mara inganci da wani marubuci ya wallafa, inda aka zargi majalisar dattawa da murda kasafin kudi.
Gaskiyar abin da ya faru
Ya ce wannan rubutu ba daga wajen Sanata Kawu Sumaila ya fito ba, sai dai kawai ya tura shi ne da kyakkyawar niyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Sanata Sani Musa:
“Rubutun ba daga hannun abokina kuma dan’uwana, Sanata Kawu Sumaila ya fito ba. Shi dai kawai ya turamin ne yana ganin gaskiya ne, saboda haka na mayar da martani daidai da abinda na fahimta. Wannan ne kawai abinda ya faru.”
Manufar da yasa ake yada maganar
Sanatan ya ce abin takaici ne yadda wasu mutane masu son tayar da zaune tsaye suke kokarin dawo da batun domin cimma wasu muggan manufofi na siyasa, musamman ganin cewa Sumaila ya koma APC.
Ya kara da cewa:
“Yanzu, wasu mutane na kokarin tayar da wannan tsohon lamari domin haddasa rigima, musamman ganin abokina Kawu Sumaila ya koma jam’iyyar APC. Amma ina tabbatar muku da cewa ni da Kawu Sumaila ba mu taba samun wata matsala ba.”
Kira ga jama’a daga bakin sanata
Ya kara da cewa ya kamata a mayar da hankali wajen gina kasa maimakon yada labaran karya da ke kawo rabuwar kai tsakanin 'yan siyasa da al’umma.
Sanatan ya bukaci al’umma da su yi watsi da irin wadannan maganganu da ya bayyana a matsayin 'shaci fadi' da ke da nufin durkusar da hadin kan da ke tsakanin 'yan majalisar da shugabannin siyasa.
Ya kara da cewa:
“Ina rokon jama’a da su yi watsi da wannan labari mara tushe. Komai siyasa ne kawai, kuma babu wani rikici tsakanina da Sanata Sumaila. Mu duka muna da burin ganin Najeriya ta ci gaba.”
Sanata Sani Musa, ya jaddada cewa ba ya da wani sabani da kowa, kuma yana ci gaba da aiki domin dorewar dimokuradiyya da ci gaban kasa.
An samu matsala a NNPP
A wani labarin, an samu rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan Sanata Kawu Sumaila daga yankin Kano ta Kudu.
Daruruwan yan jam'iyyar NNPP suka ce za su cigaba da kasancewa a cikinta kuma ba za su bi Sanata Kawu zuwa jam’iyyar APC ba.
Wadanda suka yi watsi da sauya sheka sun mamaye titin Miller inda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke zaune domin nuna biyayyarsu, cewar Tribune.
Asali: Legit.ng