Bayan Kashe Maƙudan Kuɗi, Gwamna Zai Maida Gidan Gwamnati Katafaren Otal

Bayan Kashe Maƙudan Kuɗi, Gwamna Zai Maida Gidan Gwamnati Katafaren Otal

  • Gwamnatin Abia ta bayyana cewa za ta maida sabon gidan gwamnati da ke Ogurube a Umuahia ya zama otal mai daraja
  • Kwamishinan yada labarai, Okey Kanu ya ce gidan ba ya da kayan zama, babu wurarn ajiye kaya kuma bai dace da zama ba
  • Kanu ya ce tsofaffin shugabanni sun yaudari jama’a da zargin gidan haya ne, amma sun rika biyan kansu kudin haya daga asusun gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umiahia, Abia - Gwamnatin jihar Abia ta yi magana game da sabon gidan gwamnati da aka gina.

Gwamnatin ta yi martani ne kan rade-radin da ake yaɗawa cewa an ba da gidan haya ga waɗansu tsirarun mutane.

Gwamna zai maida gidan gwamnati otal
Gwamna Alex Otti zai maida gidan gwamnati otal. Hoto: Alex C. Otti.
Asali: Facebook

Gwamna zai maida gidan gwamnati babban otal

Kwamishinan yada labarai, Okey Kanu, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai tare da manema labarai a sashen gine-ginen, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin ta ce za ta mayar da sabon gidan gwamnati da ke Ogurube a Umuahia ya zama katafaren otal.

Kanu ya kara da cewa za a gina sabon ofishin gwamna da masauki a cikin tsohon gidan gwamnatin da ake amfani da shi yanzu.

Ya karyata ikirarin cewa gidan gwamnatin da ake ciki haya ne, inda ya ce kafin yanzu, an ce gidan gwamnati haya ne, amma ba haka ba ne.

Abia: An zargi gwamnatin da ta shuɗe

Kwamishinan ya ce ginin da gwamnatin da ta gabata ta ce ta kammala da kuma kaddamar da shi ba a shirya shi don zama bane kwata-kwata.

Ya ce:

“Wannan wurin bai dace da zama ba, babu wurin ajiye kayan sakawa ko ina. Yawancin wuraren dakuna ne kawai marasa komai ciki.
“Ina mamakin wanda ya tsara wannan gini da ake kira gidan gwamnati. Shin gwamna zai iya rayuwa a irin wannan wuri?”

Gwamana zai sauya gidan gwamnati zuwa otal
Gwamnan Abia zai maida gidan gwamnati babban otal. Hoto: Alex C. Otti.
Asali: Twitter

Yadda tsarin gidan gwamnatin yake

Kanu ya jaddada cewa bene guda kacal ne ya kammala, sauran bangarorin ginin kuwa suna cikin kammalawa har yanzu.

Ya kara da cewa:

“Kawai bene na farko ne ya kammala. Sauran benen ba a gama su ba."

Ya zargi tsohon kwamishina, John Okiyi Kalu, da yada bayanan ƙarya kan ginin ba tare da bincike mai zurfi ba, Channels TV ta ruwaito.

Ya ce ginin bai da aminci kwata-kwata, inda ya ce gwamnatin da ta gabata ta yi hanzarin ginin ne kawai don ta burge jama’a.

Ya kara da cewa inda aka gina ginin yana da haɗarin tsaro domin yana tsakanin wasu gine-gine masu yawa.

Gwamna ya kauracewa gidan gwamnati

A baya, kun ji cewa Gwamnan Alex Otti na jihar Abia ya kauracewa gudanar da aiki a gidan gwamnatin inda ya koma yin aiki daga gidansa.

Gwamnan ya ce ba zai iya yin aiki a gidan gwamnatin jihar ba saboda ya lalace kuma ko kadan ginin bai dace da tsarin Abia ba.

Sai dai Gwamna Otti yi alkawarin gina “gidan gwamnati da ya dace” kafin karshen shekara, yayin da zai ci gaba da aiki daga gidansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.