A ƙarshe, Akpabio Ya Taɓo Batun Yiyuwar Yin Murabus bayan Taso Shi a Gaba

A ƙarshe, Akpabio Ya Taɓo Batun Yiyuwar Yin Murabus bayan Taso Shi a Gaba

  • Shugaban Majalisar Dattawa a Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce ba zai yi murabus ba duk da kiraye-kirayen da ake masa daga kungiyoyi da ‘yan adawa
  • Akpabio yana fuskantar zargin cin zarafin mace da kuma hannu a magudin zaɓe a 2019, amma ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya
  • A zaman majalisa, ya ce ba zai zama wanda aka zalunta bisa ƙarya ba, yana mai cewa 'Ban cikin masu sauka saboda ƙarya'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ana ci gaba da tasa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a gaba da cewa sai ya yi murabus.

Hakan bai rasa nasaba da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan game da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Akpabio ya magantu kan murabus
Godswill Akpabio ya ce ba zai yi murabus ba. Hoto: Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

An taso Akpabio a gaba ya yi murabus

Sai dai Godswill Akpabio ta yi magana kan kiraye-kirayen da ake yi masa cewa sai ya bar kujerarsa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya ƙi amincewa da maganganun mutane da ke neman ya yi murabus daga muƙaminsa.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom wanda ke fuskantar suka sosai daga jama’a a 'yan makonnin nan, ana zarginsa da cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Wasu zarge-zarge da ake yiwa Akpabio

Hakanan, ana alakanta shi da zargin magudin zaɓe a lokacin zaɓen 2019 da ya gabata wanda ya sa ake tuhumar wani Farfesa da zargin canza sakamakon zabe.

Kungiyoyin fararen hula da wasu ‘yan adawa sun bukaci ya ajiye mukami domin a gudanar da bincike cikin ‘yanci da adalci.

Akpabio ya magantu kan kiran ya yi murabus
Akpabio ya magantu kan yin murabus. Hoto: Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

Menene Akpabio ya yi kan kiran murabus?

A yayin zaman majalisa ranar Alhamis, Akpabio ya ce zarge-zargen ƙarya ne, kuma ba zai amince da a zalunce shi ba.

Ya ce:

“Da ba zan amsa ba, sai dai don ka ce wasu za su ce ka sauka. Wa ya ce zan sauka?

“Ka san, idan ka kalli Amurka, akwai bakaken fata da suka shiga gidan yari saboda ƙarya, wasu sun zauna har shekaru 25.”
“Don haka ni ban daga cikin waɗanda za su sauka saboda ƙarya ba ne. Idan aka tabbatar da ƙarya ne, sai a ce, ‘Ai ba laifi ba ne.
“Don haka idan kana da wannan a rai, ka manta da shi. Ina godiya da kalaman da kuka faɗa yau.”

Hakan ya kawo karshen masu bukatar sai Akpabio ya yi magana game da kiran yin murabus da zarge-zargen da ake masa musamman kan lamarin Natasha Akpoti-Uduaghan.

Akpabio: An bukaci Natasha ta kawo hujjoji

Kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ki janye karar da ta shigar kan Akpabio game da zargin cin zarafi, tana cewa shari'a ce za ta warware gaskiya.

Natasha ta bayyana cewa duk wasu ƙarin hujjoji da za su fito za a gabatar da su ne kawai a lokacin sauraron ƙarar ta hanyar bin doka.

Wani mai sharhi kan siyasa, Ibrahim Jamiu Adamu, ya ce rikicin Natasha da Akpabio ya na tauye hakkin al'ummar Kogi ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.