Mutane 10,000 Sun Ɓace Sakamakon Ambaliyar Ruwa a Birnin Derna Na Kasar Libya

Mutane 10,000 Sun Ɓace Sakamakon Ambaliyar Ruwa a Birnin Derna Na Kasar Libya

  • Ambaliyar ruwa mai tsananin ƙarfi ta yi sanadiyyar ɓacewar mutane aƙalla 10,000 a gabashin ƙasar Libya
  • Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata, sakamakon wata iska mai ƙarfi da ta hankaɗo ruwan teku cikin biranen yankin
  • Ya zuwa yanzu dai an yi nasarar gano gawarwakin sama da mutane 1,000 da suka rasu sakamakon ibtila'in

Derna, Libya - Akalla mutane 10,000 ne ake fargabar sun ɓata a kasar Libya ranar Talata, sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a ƙasar.

Iska mai ƙarfi da aka yi wa laƙabi da ’Storm Daniel’ ce ta haddasa ambaliyar, wacce ta lalata madatsun ruwan da ya shafe kashi daya bisa hudu na birnin Derna da ke gabashin kasar.

A wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Reuters ya fitar, ya ce a yanzu haka an gano gawarwakin mutane sama da 1,000 a Derna kaɗai.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Adadin Mutanen Da Girgizar Kasa Ta Halaka a Morocco Ya Karu Da Yawa

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane da dama a ƙasar Libya
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar ɓatan mutane aƙalla 10,000 a ƙasar Libya. Hoto: The Libya Observer
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin batan mutum 10,000 a Libya

Ambaliyar ta Libya dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin mutanen da girgizar ƙasa ta halaka a ƙasar Morocco, inda har yanzu ake ci gaba da nemo waɗanda ɓaraguzan gini suka danne.

Mahukuntan Libya sun ce adadin waɗanda suka mutu zai iya zarce abinda aka gani a yanzu, bayan da guguwar ta hankaɗo ruwan tekun Bahar Rum zuwa cikin kasar da ta shafe sama da shekaru goma tana fama da rikici.

Derna, wanda birni ne da ya yi iyaka da bakin teku, yana ɗauke da mazauna kusan 125,000, wanda suka fuskanci ibtila'in ambaliyar ruwa da ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Gawarwakin mutane sun warwatsu a wurare daban-daban

Ministan sufurin jiragen sama kuma mamba a kwamitin agajin gaggawa na gabashin ƙasar, Hichem Abu Chkiouat, ya ce gawarwakin mutane sun cika yankin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Sace Wasu Mutane Masu Yawa a Arewacin Najeriya

Ya ce gawarwakin wasu mutanen sun maƙale a jikin gine-gine, wasu kuma a yashe a kan tituna, yayin da wasu kuma ruwa ya tafi da su cikin tekun.

Ya ce akwai yiwuwar adadin mutanen da suka rasu ya kai 2,500 sakamakon yadda adadin mutanen da ba a gani ba har yanzu yake ta ƙara hauhawa kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Birnin Benghazi wanda shi ma yana a gabashin ƙasar ta Libya ne, ya fuskanci wannan ambaliyar ruwa da iskar ta haifar.

Adadin mutanen da girgizar ƙasar Morocco ta halaka ya kusa 2,500

Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan adadin mutanen da aka bayyana cewa sun rasu sakamakon girgizar ƙasar da ta afku a ƙasar Morocco.

Mazauna yankin Marrakech na ƙasar Morocco dai sun fuskanci ibtila'in girgizar ƙasa ne a ranar Juma'a da ta gabata, wacce ta janyo asarar rayuka da dukiya mai dumbin yawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ya Laƙume Rayukan Mutane Sama da 10 a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel