Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno

Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno

- Majalisar zartarwar jihar Borno a karkashin jagorancin gwamna Babagana Umara Zulum ta amince da tallafawa mafarauta da kungiyar CJTF

- Kazalika, Zulum ya amince da fitar da wasu kudade domin gina hanyoyi da ajuzuwan karatu na zamani a wasu makarantu

- A cewar kwamishinan yada labarai, majalisar zartarwar ta sake amincewa da fitar da biliyan 1.6 don wasu gine-gine a asibitin koyarwa na jihar

Majalisar zartarwa ta jihar Borno a karkashin jagorancin gwamna Babagana Zulum ta amince da ware ₦352 don tallafawa mafarauta da ƙungiyar yan sa-kai ta CJTF da ke yaƙi da hare-haren ƙungiyar Boko Haram.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Babakura Abba-Jato, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Maiduguri.

Abba-Jato ya kara da cewa amincewar ta biyo bayan mitin da kwamitin zartarwa ya yi wanda gwamnan Zulum ya jagoranta, kamar yadda rahotanni suka rawaito kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya sanar.

KARANTA: Zugar mambobin PDP ta dunguma zuwa jam'iyyar APC a Zamfara

Kwamishinan ya ƙara da cewa, akwai wasu kuɗaɗe da ake sa ran gwamnan zai amince da fitar da su, miliyan 658 don gyaran titin da ya tashi daga Maiduguri zuwa Damboa da kuma miliyan 231 don cigaba da aikin titin Banisheikh.

Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno
Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno @Vanguard
Source: Twitter

Ya ce, miliyan 237 an ware ta ne don gina titin daga Ramat zuwa Wulari da hanyar ruwa dake cikin garin Maiduguri.

KARANTA: Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria

A cewar kwamishinan, majalisar zartarwa ta jihar ta sake amincewa da fitar da biliyan 1.6 don wasu gine-gine a asibitin koyarwa na jihar.

"Gina dakunan ajuzuwa mai hawa biyu a kauyen Buratai dake karamar hukumar Biu zai laƙume miliyan 253, yayin da miliyan 84 aka amince da kashe ta wajen sayo kayan gwaje-gwaje da kayan aiki na zamani a kwalejin koyar da sana'a dake Njimtola," Cewar Kwamishinan.

A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel