Jihohi 6 da Shugaba Tinubu Ya Ziyarta bayan Hawansa Mulki
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci wasu daga cikin jihohin Najeriya bayan rantsar da shi a kan mulkin Najeriya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Shugaba Bola Tinubu dai ya kama rantsuwar aiki ne a ranar, 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Facebook
Jihohin da Bola Tinubu ya ziyarta
Wasu daga cikin jihohin da Shugaba Tinubu ya ziyarta, ya je ne domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnoninsu suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ziyarar dai, shugaban ƙasan yana samun tarba daga wajen jam'ian gwamnati da sauran al'umma.
Ga jerin jihohin da Tinubu ya ziyarta:
1. Jihar Legas
A ranar Talata, 27 ga watan Yunin 2023, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ziyarci jihar Legas.
Shugaba Tinubu ya je jihar Legas ne domin bukukuwan babbar Sallah na shekarar 2023, cewar wata sanarwa da aka sanya a shafin statehouse.gov.ng
Zuwan nasa shi ne ziyarsa ta farko zuwa Legas tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Ya samu tarba daga wajen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, muƙaddashin Sufeto Janar na ƴan Sanda, Olukayode Egbetokun.
Sauran sun haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, sanatoci da ƴan majalisarwakilai daga jihar Legas, da kuma shugabannin jam’iyyar APC.
2. Jihar Ogun
A ranar Alhamis, 29 ga watan Yunin 2023, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Ogun inda ya tsaya a fadar Sarkin Ijebu, Awujale, Oba Sikiru Kayode Adetona.
Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya tarbi shugaban ƙasan a filin wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode, cewar rahoton tashar Channels tv.
Shugaba Tinubu ya samu rakiya daga mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
3. Jihar Neja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki a jihar Neja a ranar Litinin, 11 ga watan Maris 2024.
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka na musamman waɗanda Gwamna Umar Bago ya aiwatar a jihar, cewar wata sanarwa da aka sanya a shafin statehouse.gov.ng
A lokacin ƙaddamarwar, shugaban ƙasan ya bayyana shirin gwamnatinsa na kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a fadin jihar.
Yayin da yake roƙon gwamnonin jihohi da su bayar da filaye, Tinubu ya ce zai ƙirƙiri wani shiri da zai kawo ƙarshen rikicin cikin makonni biyu zuwa uku.
4. Jihar Borno
A ranar Litinin, 16 ga watan Satumban 2024, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyarar jaje a jihar Borno, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Shugaba Tinubu ya ziyarci Borno ne domin jajantawa gwamnatin jihar da al'umma bisa ibtila’in ambaliya da ya ritsa da su.
Bayan isarsa birnin Maiduguri da misalin ƙarfe 3:40 na rana, ya wuce wani sansani da aka kafa domin kula da waɗanda ambaliyar ta shafa.
A sansanin, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa da waɗanda suka rasa matsuguni cewa gwamnatinsa za ta tallafa musu.
Tawagar da ta yi masa rakiya ta haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ministan Noma, Abubakar Kyari, da wasu masu taimaka masa.
5. Jihar Enugu
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa jihar Enugu a ranar 4 ga Janairu, 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.
Mai girma Bola Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Gwamna Peter Mbah ta aiwatar a jihar.

Asali: Twitter
A cewar wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha, Farfesa Chidiebere Onyia, ya fitar a ranar Juma’a, Shugaban zai ƙaddamar da Cibiyar Taro ta Ƙasa da aka gina a Enugu.
Ayyukan da shugaban ƙasan ya ƙaddamar sun haɗa da makarantu 30 na zamani da aka kammala cikin guda 260 da za a yi a faɗin mazaɓu 260 na jihar.
Sauran sun haɗa da cibiyoyin lafiya matakin farko guda 60 da aka kammala daga cikin 260 da ake ginawa a cikin kowace mazaɓa a faɗin jihar.
6. Jihar Katsina
A ranar Juma'a, 3 ga watan Mayun 2025, Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki a jihar Ƙatsina, cewar rahoton Premium Times.

Asali: Facebook
A yayin ziyarar ta sa ya ƙaddamar da titin Eastern Bypass da kuma cibiyar noma ta zamani wadda gwamnatin Gwamna Dikko Radda ta gina.
Hakazalika, shugaban ƙasan ya halarci ɗaurin auren ɗiyar Gwamna Dikko Radda tare da angonta.
Tinubu ya koka kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan ƙalubalen rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa dole ne a magance matsalar idan har ana son a jawo masu zuba hannun jari zuwa cikin ƙasar nan.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da fasahohi na zamani domin ƙwato dazukan ƙasar nan da ke hannun ƴan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng