Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Shugaban Kasa a Minna, An Faɗi Abin da Ya Faru

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Shugaban Kasa a Minna, An Faɗi Abin da Ya Faru

  • Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, sun yi wata ganawar sirri a Minna ranar Litinin
  • Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja ne kaɗai ya shiga wurin da jiga-jigan biyu suka tattauna kan muhimmin batutuwa
  • Shugaban ƙasa Tinubu ya je jihar Neja ne ziyarar aiki ta kwana ɗaya inda ya kaddamar da ginin da aka sabunta na filin jirgin saman Minna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Minna, jihar Neja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Bola Tinubu ya bar wurin bikin kaddamar da aikin da Gwamna Mohammed Umaru Bago ya aiwatar a Minna, babban birnin jihar Neja, ya wuce kai tsaye zuwa gidan IBB.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

Shugaba Tinubu ya gana da IBB.
Abin da Tinubu ya tattauna da IBB a Minna Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya jihar Neja a ranar Litinin 11 ga watan Maris, domin kaddamar da aikin sabunta ginin filin jirgin sama a Minna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sauya sunan filin jirgin saman Minna

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, an canza sunan filin sauka da tashin jirgin saman zuwa filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu na ƙasa da ƙasa.

Bayan kaddamar da wannan aiki, shugabam ƙasa Tinubu ya kuma yi wasu ayyukan duk a jihar Neja da ke Arewa ta tsakiya.

An tattaro cewa shugaba Tinubu ya kai ziyara tare da shafe sama da sa’a guda yana tattaunawa IBB kan batutuwan da suka shafi halin da kasar nan ke ciki.

Rahoto ya nuna cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ne kadai ya halarci taron na sirri tsakanin shugabannin biyu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gwamnonin jihohi sabon umarni kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Wane batu Shugaba Tinubu ya tattauna da IBB?

An bayyana cewa, tsohon shugaban kasa Babangida, “ya ​​ba shi (Tinubu) shawara a matsayinsa na dattijon ƙasa kuma ya jaddada bukatar yin gaggawar aiwatar da jawabinsa.”

IBB ya bada shawarar cewa duk wani shiri na gwamnati ya kamata a rika bari yana kai wa ga talaka, ya kuma yi alkawarin cewa kofarsa a buɗe take a kowane lokaci ga dukkan shugabanni.

Tinubu na zargin Buhari ne ya jefa Najeriya cikin wahala?

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya nesanta kansa daga cikin muƙarraban gwamnatinsa da ke zargin Muhammadu Buhari, da jefa Najeriya cikin kakanikayi a mulkinsa.

Yayin da ya ziyarci jihar Neja, shugaban kasar ya ce ba halayyarsa ba ce ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifin rashin tsaro da matsin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel