An Iso Wurin: EFCC na Zargin Mele Kyari da Wasu a NNPCL kan Badakalar N80bn
- EFCC na binciken tsofaffin shugabannin NNPC da wasu daraktocin matatun mai bisa zargin batar da $2.96bn na gyaransu
- Hukumar ta kama wasu daga cikin tsofaffin daraktocin, ciki har da Ibrahim Onoja na Port Harcourt da Efifia Chu na Warri
- Binciken ya nuna an ware $1.56bn ga Port Harcourt, $740m ga Kaduna, da $657m ga Warri, amma ba a yi amfani da kudin ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) na binciken tsofaffin shugabannin Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL).
Daga cikin wadanda ake tuhuma akwai Mele Kyari da daraktocin matatun mai da aka kora daga aiki bayan sauye-sauye.

Asali: Twitter
Wata majiya daga EFCC da ta nemi a boye sunanta ta tabbatar da cewa ana binciken wasu manyan jami’ai masu mukami a kasar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL: An taso Kyari kan badakalar $1.5bn
Wannan na zuwa ne bayan wata kungiya ta kwararru da 'yan ƙasa masu kishin Najeriya ta bukaci a binciki tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari, kan kashe $1.5bn.
Kungiyar ta yabawa Bola Tinubu bisa sauke Kyari, tare da cewa an zuba makudan kudi a gyaran matatar mai ba tare da haifar da 'da mai ido ba.
Ta ce akwai buƙatar kwakkwaran bincike kan bacewar ganga miliyan 89 na danyen mai da kuma yarjejeniyar mai da kamfanin Matrix.

Asali: Facebook
Musabbabin binciken EFCC a kamfanin NNPCL
Binciken na duba yadda aka yi da kudin gyaran matatun mai, wadanda tuni suka dade suna fama da matsalolin aiki da gyara.
Binciken farko ya nuna an ware $1.56bn a matatar Port Harcourt, $740m zuwa ga Kaduna, da $657m ga Warri da ke jihar Delta a Kudu maso Kudancin Najeriya.
An riga an kama wasu, ciki har da tsohon daralektan matatar Port Harcourt, Ibrahim Onoja, da Efifia Chu na Warri.
Rahotanni sun nuna daya daga cikin tsofaffin daraktocin ya kwashe fiye da sati daya a hannun EFCC bayan an gano makudan kudi a asusunsa.
Zargin badakala: EFCC ta ba NNPCL umarni
Wannan badakala ta tada hankali sosai, har wasu ke cewa zata iya zarce ta Godwin Emefiele wajen girma da kuma yadda lamarin ya girgiza kasa.
Har lokacin hada wannan rahoto, mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, bai bayar da wani karin bayani kan binciken ba.
A yanzu haka, EFCC ta bukaci NNPCL da ta mika mata cikakken bayanin kudi da albashi da sauran kudaden alawus domin ci gaba da bincike.
EFCC ta musanta katsaladan daga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan zargin cewa Bola Tinubu na shiga lamarin bincikensu.
Ola Olukoyede ya musanta cewa shugaban ƙasan yana amfani da hukumar wajen muzgunawa ƴan jam'iyyun adawa.
Shugaban na EFCC ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya fi mayar da hankali wajen ganin shugabannin ma'aikatu sun sauke nauyin da aka ɗora musu.
Asali: Legit.ng