An Naɗa Sheikh Bashir Aliyu a Matsayin Shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya

An Naɗa Sheikh Bashir Aliyu a Matsayin Shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya

  • Sheikh Bashir Aliyu Umar daga jihar Kano ya zama sabon shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya (SCSN)
  • Sakataren Majalisar, Malam Nafi'u Baba Ahmed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannunsa
  • Naɗin Dr. Bashir na zuwa ne bayan rasuwar shugaban Majalisar, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) ta sanar da naɗin Sheikh (Dr.) Bashir Aliyu Umar, a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa.

Wannan mataki na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, wanda ya koma ga Allah a ranar Litinin da ta wuce.

Dr. Bashir Aliyu Umar.
Majalisar Shari'ar Musulunci ta nada Sheikh Bashir Aliyu a matsayin shugabanta Hoto: Dr. Bashir Aliyu Umar
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Sakataren Majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmed, ne ya tabbatar da naɗin Sheikh Bashir Aliyu a wata sanarwa da ya sa wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana rasuwar Sheikh Hadiyatullah a matsayin babban rashi ga Majalisar da kuma al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

An naɗa Dr. Bashir Aliyu shugaban SCSN

Yayin da yake addu’a Allah Ya gafarta masa Ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus, Malam Nafiu ya ce an naɗa Dr. Bashir ne bisa kundin tsari da dokokin da Majalisar ta kafa.

“An amince da naɗin Mataimakin Shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar OON, a matsayin sabon Shugaba.
"Muna da cikakken yakinin cewa jagoranci, ilimi da hazaƙar da Allah ya ba Sheikh Dr. Bashir za su taimaka wajen ciyar da tsarin Shari’ar musulukci da adalci gaba.
"Za a sanar da sabon Mataimaki a nan gaba, In Shaa Allah. Muna rokon addu’o’i da goyon bayan al’umma domin ci gaba da gudanar da ayyukan da Majalisar ke yi na yada shari'ar Musulunci a faɗin Najeriya.”

Taƙaitaccen bayani ka Dr. Bashir Aliyu Umar

Fitaccen malamin musulunci daga Kano, Dr. Bashir sananne ne a fagen ilimin addinin Musulunci da kuma tsarin harkokin kuɗi a Musulunci a Najeriya.

Yana da digirin farko da na biyu har zuwa digirgir (Ph.D.) a fannin Hadisi da Ilimin Addinin Musulunci daga Jami’ar Musulunci ta Madina.

Dr. Bashir Aliyu Umar.
Sheikh Bashir Aliyu Umar babban malamin musulunci ne a Najeriya Hoto: Dr. Bashir Aliyu Umar
Asali: Facebook

Sheikh Bashir Aliyu Umar ya rike mukamai daban-daban a ƙungiyoyin da ke da nasaba da Shari’a da harkar banki na Musulunci a gida da wajen Najeriya.

Daga ciki har da kwamitin ba da shawara na shari’a na Stanbic IBTC Bank da kuma Majalisar Masana Harkokin Bankin Musulunci ta Babban Bankin Najeriya (CBN).

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar shugabn SCSN

A baya, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana Marigayi Sheikh Hadiyyatullah a matsayin malami na gari mai tsoron Allah.

Shugaba Tinubu ya ce malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa addinin Musulunci hidima da kuma taimaka wa al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262