Ta Faru Ta Kare: Kotu Ta Yankewa Sojan Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Ta Faru Ta Kare: Kotu Ta Yankewa Sojan Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

  • Wata kotun soja a jihar Enugu ta yanke wa wani soja, Adamu Mohammed hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe budurwarsa
  • Shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, ya ce sojan ya aikata laifin da ya ci karo da sashe na 106 (a) na dokar sojoji, Cap A20 LFN 2004
  • Haka zalika, kotun ta yanke wa wani soja, Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 bisa laifin aikata fashi da makami a wasu shaguna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Wata kotun soja ta musamman (GCM) a jihar Enugu, ta yanke wa wani soja mai suna Adamu Mohammed hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun GCM da ke a cikin hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta 82, ta yanke hukuncin kisa ga Adamu ne bisa kama shi da laifin kashe budurwarsa.

Kotu ta yanke wa wani soja hukuncin kisa ta hanyar rataya a Enugu
Hafsan rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede a wata ziyara da ya kai Sokoto. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Kotun sojoji ta yanke wa soja hukunci a Enugu

Jami’in watsa labarai na runduna sojojin ta 82, Laftanal Kanal Jonah Unuakhalu ya bayyana hukuncin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da ya fitar a Enugu, Laftanal Kanal Jonah ya bayyana cewa kotun GCM ta yanke hukuncin ne bayan cikakken bincike kan laifin kisan.

Kotun sojar ta kunshi mambobi 11, kuma an kafa ta ne a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, bisa umarnin kwamandan runduna ta 82, Manjo Janar Oluyemi Olatoye.

Kotu ta yanke wa soja hukuncin kisa a Enugu

Shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, ya ce bayan sauraron shaidu da nazari kan ayyukan Adamu Mohammed, kotun ta yanke masa hukuncin kisa saboda kashe budurwarsa.

Birgediya Janar Sadisu ya ce laifin yana karkashin sashe na 106 (a) na dokar sojojin Najeriya, Cap A20 LFN 2004, kuma hukuncin ya yi daidai da abin da doka ta tanada.

Ya kara da cewa kotun ta yi la’akari da tarihin aikin sojan da rokon sassauci daga shi da lauyansa, amma dole ne a tabbatar da adalci ga mamaciyar.

Shugaban kotun ya ce:

“Don haka, kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da aka gurfanar, mai lamba 21NA/80/6365, Pte Adamu Mohammed.”
Kotu ta daure wani sojan Najeriya shekaru 10 a gidan yari
Hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Kotu ta daure soja shekaru 10 a Enugu

Haka zalika, kotun ta daure wani soja, Abubakar Yusuf, shekaru 10 a gidan yari bisa laifin fashi da makami a wani wani rukunin shaguna a Enugu.

Birgediya Sadisu ya ce an kama Yusuf da laifin fashi, wanda doka ta tanadi hukuncinsa a karkashin sashe na 107(1)(b) na dokar sojoji, Cap A20 LFN 2004.

Duk da rokon sassauci daga lauyansa, Sadisu ya ce kotun ba ta cimma matsaya guda daya da ake bukata domin yanke mafi tsananin hukunci da doka ta tanada ba.

Saboda haka, bisa sashe na 140 (3) na dokar sojoji, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.

Ya ce yanzu ana jiran tantancewa tare da amincewar hukumomin da suka dace kafin aiwatar da hukunce-hukuncen da aka yanke wa sojojin, wanda hakan ke nuna ƙarshen shari’ar.

Matsayar doka da goben aiki a Najeriya

A wannan hukunci da kotun soja ta yanke a Enugu, an tabbatar da aiwatar da doka ba tare da nuna son kai ba.

Hukuncin kisa da aka yanke wa Pte Adamu Mohammed ya fito ne sakamakon kisan da ya aikata, wanda ya girgiza al'umma. Kotun ta ce dole ne a kare mutuncin rayuwa da doka ta tanada.

Haka kuma, hukuncin ɗaurin shekaru 10 da aka yanke wa Abubakar Yusuf ya nuna cewa rundunar soji ba za ta lamunci aikata laifuka ba, ko daga dukkansu. Wannan hukunci ya zama darasi ga sauran jami’an soja da ke cikin aiki..

Kotu ta daure babban Janar kan sata

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata kotu da ke zamanta a Abuja, ta samu wani babban soja, Manjo Janar Umar Mohammed, da laifin satar kuɗaɗen kamfanin soji na NAPL.

An ce rundunar sojin Najeriya ce ta gurfanar da Manjo Janar Umar kan tuhume-tuhume 18 da suka haɗa da amfami da takardun jabu, almubazzaranci da kuɗaɗe da sauransu.

A hukuncin kotun, an bayar da umarnin a ɗaure Umar shekaru biyar kan wasu laifuffukan da ake tuhumarsa da su, yayin da wasu laifuffukan ke da hukuncin ɗaurin shekara bakwai da biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.