Da duminsa: Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa

Da duminsa: Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa

- Bayan watanni shida da aikata laifi, kotu ta yankewa soja hukuncin kisa

- Kotun ta yankewa wasu sojin daban hukuncin dauri a gidan kaso kan wasu laifukan daban

Kotun soji dake zamanta a Maidiguri, jihar Borno ta yankewa jami'in soja, Azunna Maduabuchi hukuncin kisa kan laifin kisan kwamandansa, Laftanal Babakaka Ngorji.

Kotun ta yanke a kashe shi ta hanyar harbi, Channels Tv ta ruwaito.

An gurfanar da Maduabuchi ne bayan da ya budewa Babakaka Ngorji wuta a watan Yulin 2020 a sansaninsu dake karamar hukumar Bama a jihar Borno don ya hanashi zuwa gida.

Kotun dake Maimalari Cantonment, ta kamashi da laifin kisan kuma ta yanke masa hukuncin kisa.

Sauran sojojin da aka kama da laifin kisa sun samu hukuncin dauri shekaru a gidan kaso.

Wadanda aka yankewa hukumar sune Sajen Sani Ishaya, hukucin shekaru hudu; Bidemi Fabiyi, hukuncin shekaru biyu; sai kuma Private Musa Bala da Abdulrasheed Adamu, da aka yankewa hukuncin shekara daya.

Wani Soja kuma mai suna Mohammed Kudu da aka tuhuma da laifin kashe wani yaro a wani bikin daurin aure ya samu daurin shekaru uku a gidan kaso.

Hakazalika an ragewa Lance Kofura Aja Emmanuel matsayi kan laifin cin zarafi. Yanzu ya koma Private.

KU KARANTA: Za ku iya cira kudinku kowani lokacin: FG yayinda take shirin aron kudin da mutane suka ajiye a banki

Da duminsa: Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa
Da duminsa: Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

Mun kawo muku a bayan cewa wani Sojan Najeriya dake 202 Bataliya dake Bama jihar Borno ya bindige Laftana kwamandarsa, Bakaka Ngorgi, kan rashin bashi daman tafiya domin magance wasu matsalolin da suka tattari rashin samun albashinsa na tsawon watanni takwas.

Sojan ya budewa shugabansa wuta ne yayinda magana a wayar salula ranar Laraba a hedkwatar.

Ba tare da bata lokaci ba aka damke Sojan yayinda aka garzaya da agwar hafsan da ya kashe zuwa asibitin 7div.

Harbin ya tayarwa Sojoji da Hafsoshin 202 Bataliya hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel