Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula

Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula

Wata kotun sojoji da ke zama a Abuja a ranar Laraba ta yanke wa wani soja hukuncin shekaru 55 a gidan yari a kan kisan kai, balle wa tare da sata.

Sojan mai mukamin Lance Corporal, an zargesa da kashe wani mutum mai suna Bello Abdullahi Aliyu tare da kwace masa mota a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Lance Corporal Ibrahim Babangida ya aikata laifin ne a 2014.

Aliyu a wancan lokacin ma'aikacin kungiyar kiwon lafiya ta duniya ne a jihar.

An zargi kofur Babangida da satar waya da kudi N600,000 daga wurin mutane da dama a lokuta mabambamta.

Solacebase ta ruwaito cewa shugaban GMC, Manjo Janar Priye Fakrogha yayin karanta hukuncin bayan sauraron bayanai daga masu gurfanarwa da masu kare kansu, ya ce wanda aka kama da laifin an yanke masa hukuncin shekaru 40 a gidan yari saboda kisan kai.

Janar Fakrogha ya kara da cewa, Babangida zai yi zaman gidan yari na shekaru biyar sakamakon kin amsa laifinsa da yayi har sau uku.

PRNigeria ta gano cewa, hukuncin GCM din zai tabbata ne bayan hukumar sojin kasa ta Najeriya ta amince da shi.

Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula
Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula. Hoto daga Solacebase
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zulum ya mayar da mutum 560 gida bayan harin Auno

A wani labari na daban, wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta yanke wa wani tsoho hukuncin kisa ta hanyar jifa sakamakon laifin yi wa karamar yarinya fyade da aka kama shi da shi.

Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, alkalin kotun, ya ce za a kashe tsohon mai suna Mati Audu ta hanyar jifa. Kotun ta samu Mati Audu mai shekaru 70 da laifin yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 12 fyade a karamar hukumar Tsanyawa.

Tsoho Mati Audu ya tabbatar wa da kotun cewa shi ya aikata laifin fyaden. An dage shari'ar har sau hudu inda alkalin ya ba shi dama ko zai sauya ra'ayinsa da shaidarsa.

Amma kuma, a kowanne karo da aka koma zaman kotun, ya jaddada cewa shi ya yi wa karamar yarinyar fyade inda ya bukaci a yafe masa.

Bayan nan, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola ya karanto sassan Al-Kur'ani mai tsarki da kuma wasu hadisan Manzon Allah wadanda suka nuna girman laifin da Mati Audu ya aikata.

Daga nan ya yanke hukuncin kisa ta hanyar jifa kamar yadda sashi na 127 na kundin tsarin shari'ar Musulunci na jihar Kano ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel