Da Gaske Rufin Majalisar Tarayya da Aka Gyara kan N38bn Yana Yoyo? An Samu Bayanai

Da Gaske Rufin Majalisar Tarayya da Aka Gyara kan N38bn Yana Yoyo? An Samu Bayanai

  • Shugaban kamfanin 'Laralek Ultimate Construction', ya musanta rahoton cewa rufin Majalisar Tarayya yana yoyo bayan ruwan sama
  • Olalekan Adebiyi ya kara da cewa rufin da aka yi amfani da kayan Amurka aka gyara shi ne, kuma ba zai iya barin ruwa ya shiga ba
  • Adebiyi ya ce abin da ya faru shi ne ruwa ya shigo ta kananan tagogi, ba wai rufin kwanon ne ya ke yoyo ba kamar yadda aka ruwaito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban Kamfanin 'Laralek Ultimate Construction', Olalekan Adebiyi, ya yi magana kan zargin yoyo a rufin majalisar tarayya.

Adebiyi ya karyata rahotannin da ke cewa rufin ginin Majalisar Tarayya ya fara yoyo bayan ruwan sama mai karfi a Abuja.

An ƙaryata cewa rufin majalisa na yoyo a Abuja
kamfanin da ya yi aikin gyaran majalisa ya ƙaryata cewa rufin kwanon na yoyo. Hoto: House of Representatives.
Asali: Twitter

Sai dai Adebiyi, cikin wata hira ta wayar tarho da 'yan jarida, ya ce rahoton karya ne kuma binciken da aka yi ya tabbatar da babu yoyo a rufin, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da ake yaɗawa kan rufin majalisa

Wata kafar yada labarai a yanar gizo ta ruwaito cewa ruwan sama mai karfi da aka yi ranar Juma'a ya lalata aikin gyaran da aka yi daga 2022 zuwa 2024.

Rahoton ya ce wasu ma'aikatan Majalisar sun ce da kamfanin Julius Berger ne ya yi aikin, da ba za a samu matsalar yoyo a rufin ba.

Hakan ya biyo bayan cewa an kashe aƙalla makudan kudi har N38bn domin gyaran ginin majalisar cikin shekaru biyu.

Martanin kamfani kan zargin lalacewar rufin majalisa

Sai dai Adebiyi ya bayyana cewa a rufin da aka gyara, an yi amfani da wani rufin roba ne daga Amurka, wanda ya rufe kofofin ruwa gaba daya kuma ba zai fashe ba.

Ya ce:

"Rahoton ba gaskiya ba ne, kuma idan Julius Berger ne ya yi aikin, da babu irin wannan labarin karya da ake yadawa a yanzu.

"Ban fahimci dalilin da yasa wasu 'yan Najeriya ke zama makiyan 'yan uwansu ba, ba tare da wani dalili mai kyau ba."
An ƙaryata labarin cewa rufin majalisa na yoyo
Kamfanin da ya yi aikin majalisar tarayya ya ƙaryata cewa rufin ginin na yoyo bayan tafka ruwan sama. Hoto: Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

Gaskiyar abin da ya faru a majalisa

Adebiyi ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne ruwa ya shiga ta kananan tagogi na saman ginin, ba ta hanyar fashewar rufi ba.

Ya ce:

"Rahoton ba shi da wani hoto da ke nuna inda rufin ke yoyo, kuma hakan rashin kwarewa ne da rashin da'a ga aikin jarida.
"Rahoton karya ne, babu wani fashewar rufi, mun yi aikin kirki kuma muna da tabbacin cewa za a gane gaskiya."

'Yan majalisa a PDP sun marawa Tinubu baya

Kun ji cewa gamayyar ƴan majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Rivers, sun amince da sake goyawa Bola Tinubu baya a zaɓen 2027.

Mambobin ƙungiyar yan majalisar sun bayyana cewa za su yi aiki tuƙuru domin ganin shugaban ƙasan ya sake samun mulki a karo na biyu.

Sun jinjinawa shugaban ƙasan kan yadda yake yabawa da irin ƙoƙarin da Nyesom Wike yake yi a muƙaminsa na ministan Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.