Dan China Ya Kunsawa Budurwa Yar Najeriya Ciki Sannan Ya Tsere, Bidiyon Yaron Ya Dauka Hankali

Dan China Ya Kunsawa Budurwa Yar Najeriya Ciki Sannan Ya Tsere, Bidiyon Yaron Ya Dauka Hankali

  • Wani dan China da ke zama a Shagamu, jihar Ogun ya yi wa wata budurwa yar Najeriya ciki, kuma ta haihu
  • Wani bidiyo ya nuno matashiyar da danta wanda ke da kalar fatan jiki da suma irin na yan China
  • An bayyana cewa mutumin ya bukaci matar ta siyar masa da yaron lokacin da yake shirin komawa kasarsa wato China

Wani dan China wanda ke zama da aiki a Najeriya ya yi wa wata budurwa yar Najeriya ciki, kuma ta haihu.

Mutumin ya kama soyayya da matashiyar a Shagamu, jihar Ogun, inda yake aiki, kuma soyayyarsu ta kai ga samun juna biyu.

Dan China ya gudu ya bar yar Najeriya da dansa
Dan China Ya Kunsawa Budurwa Yar Najeriya Ciki Sannan Ya Tsere, Bidiyon Yaron Ya Dauka Hankali Hoto: Twitter/@Yorubaness/@KoikiMedia.
Asali: Twitter

Matashiyar ta raini cikin sannan ta haifi yaro wanda ke da suffofi irin na yan China.

Dan China ya yi watsi da uwar dansa, ya koma China

Kara karanta wannan

Yar Shekaru 36 Ta Ce Maza Na Rabuwa Da Ita Idan Suka Gane Ita Budurwa Ce Bata San Namiji Ba

Abun bakin ciki, an rahoto cewa mutumin ya yi watsi da matar da yaronsu inda ya koma kasarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto cewa mutumin ya dage lallai zai siyi yaron da kudi, lamari da mahaifiyar dan ta ki yarda da shi.

Ya bar kasar ba tare da ya dauki dan da mahaifiyarsa ba. Wani bidiyo da @KoikiMedia ya wallafa ya nuno uwa da dan nata.

An rubuta a bidiyon:

"Wani dan China ya yi wa wannan matashiyar ciki a wani wuri a kan hanyar Sagamu Abeokuta. Soyayyarsu ta tafi daidai har sai lokacin da zai koma kasarsa, sannan ya bukaci ta sayar masa da jaririn, idan ba haka ba zai dauki dawainiyarsa ba. Ta ki sayar da jaririn, shi kuwa ya yanke shawarar yanke alaka da uwa da dan."

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Ba Zata: Bidiyon Yadda Mai Kamfani Ta Gwangwaje Ma'aikacinta da Kyautar Mota, Da Keke Yake Hawa

Jama'a sun yi martani ga bidiyon budurwa da dan China ya yi wa ciki

@MoSuo777 ta ce:

"Babu wani abu da za a yi. Ya kamata yan matan Najeriya su daina firgita da rawar jiki idan suka ga mutanen Asiya da fararen fata."

@NkyEzenwa ta yi martani:

"Shin ta kai rahoto ga yan sanda? Idan ta kai, me yasa suka bar shi ya bar kasar?"

Na shekara daya ba wanka: Budurwa ta koka a bidiyo

A wani labarin kuma, wata matashiya mara galihu daga jihar Ogun mai suna Mary, ta bayyana tsananin matsin rayuwa da take fuskanta duk kwanan duniya.

Da take jawabi a harshen turanci mai kyau, Mary ta bayyana kangin rayuwa da take fuskanta ciki harda cewa bata yi wanka ba tsawon shekara daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel