Sojoji Sun Bindige ’Yan Sa Kai da Fararen Hula Yayin Harin Filato? Gaskiya Ta Fito

Sojoji Sun Bindige ’Yan Sa Kai da Fararen Hula Yayin Harin Filato? Gaskiya Ta Fito

  • Wasu kungiyoyi a jihar Filato sun zargi rundunar sojoji da kisan wasu fararen hula a jihar yayin wani hari a ranar Juma’a
  • Rundunar ta karyata wannan labari inda ta ce kawo daukin gaggawa da jami’anta suka yi ne ma ya taimaka wurin dakile harin
  • Hakan ya biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu a Bokkos da ke karamar hukumar Mangu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Plateau – Rundunar sojojin Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa jami’anta sun harbi fararen hula a jihar Filato.

Sojojin sun karyata labarin inda suka ce babu kamshin gaskiya ko kadan a lamarin da ya afku a Bokkos da kae karamar hukumar Mangu.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga ta ɓarke yayin da sojoji suka kashe bayin Allah da dama a Arewacin Najeriya

Sojoji sun yi martani kan zargin harbin fararen hula a Filato
Sojoji ƙaryata jita-jitar cewa sun bindige wasu fararen hula a Filato. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Ana zargin sojojin da tafka ta'asa

A ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu akalla mutane 10 suka rasa ransu bayan ‘yan bindiga sun farmaki kauyukan Mandar Shar da Kopnanie a kananna hukumomi biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, harin ya yi sanadin samun raunuka ga mutane da dama da kuma asarar dukiyoyin al’umma.

Wata kungiya, Bokkos Cultural Development Council (BCBC) da wata daban sun zargi sojojin da harbe wasu fararen hula.

Kungiyoyin sun yi zargin cewa sojojin sun bindige ‘yan sa-kai guda hudu da suka yi kokarin ba da gudunmawa a dakile harin.

Wane martani rundunar ta yi kan zargin?

Sai dai rundunar ta bakin jami’in yada labarai na ‘Operation Safe Haven’, Samson Zakhom ya karyata labarin a shafin Facebook.

Zakhom ya bayyana haka ne a jiya Litinin 15 ga watan Afrilu inda ya ce ba su da alaka da abin da ake zarginsu.

Kara karanta wannan

Daliban jami'ar tarayya ta Gusau da aka sace sun samu 'yanci

Ya ce daukin gaggawa da rundunar ta kai nema ya taimaka wurin nasarar dakile harin tare da ceto mutane da dama.

Sojoji sun karyata nuna wariya

A baya, kun ji cewa rundunar sojoji ta karyata cewa ta na nuna wariya tsakanin sojojin Arewa da Kudancin kasar.

Martanin rundunar na zuwa ne yayin da wasu ke zargin ta na fifita ‘yan Arewa idan aka kwatanta da takwarorinsu na Kudu.

Sojojin sun yi fatali da lamarin inda suka ce a kullum burinsu shi ne kawo zaman lafiya a kasar ba tare da nuna bambanci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel