Ayarin Matar Shugaban Ƙasa Ya Gamu da Hatsari har An Rasa Rai? Ƴan Sanda Sun Yi Bayani

Ayarin Matar Shugaban Ƙasa Ya Gamu da Hatsari har An Rasa Rai? Ƴan Sanda Sun Yi Bayani

  • Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton cewa motar ayarin matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta kaɗe wata yarinya a jihar Ondo
  • Kakakin ƴan sandan jihar, Olusola Ayanlade ya ce a bayanan da suka samu daga shaidu, wani direba ne ya buge yarinyar har ta mutu
  • Ya ce tuni rundunar ta fara kokarin binciko direban da ya yi ajalin yarinyar, inda ya nemi jama'a su taimaka wa ƴan sanda da bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ondo ta musanta rahotannin da ke cewa hatsari ya rutsa da ayarin motocin matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu.

An tattaro cewa hatsarin, wanda ake zargin ya rutsa da motar ayarin matar Tinubu, ya yi ajalin wata yarinya yar shekara bakwai a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Yan sanda.
Yan sanda sun musanta raɗe-raɗin da ake cewa motar ayarin matar shugaban kasa ta yi ajalin wata yarinya a Ondo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Amma rundunar ƴan sanda ta ce babu ayarin matar shugaban ƙasa a hatsarin wanda ya auku ranar Alhamis, 17 ga watan Afrilu. 2025, rahoton Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Ondo, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Motar ayarin matar Tinubu ta yi hatsari?

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa matar shugaban kasar na ziyarar aiki a jihar domin raba kayan tallafi da na sana’o’i ga mata da mabuƙata.

Ayanlade ya ce:

“Binciken farko da kuma bayanan da shaidu suka bayar sun tabbatar da cewa wani direban mota da ba a san shi ba, da ke tuka wata motar Lexus fara mara lamba ne ya kaɗe yarinyar.
"Amma ba wata motar da ke cikin ayarin matar shugaban kasa ba ce ta buge yarinyar. Wani direba ne da ba'a san shi ba.

Ƴan sanda sun yi bayanin abin da ya faru

Kakakin ƴan sandan ya kara da cewa a bayanan da suka samu daga wani ganau, an bi direban motar da ya buge yarinyar a babur saboda ya nuna ba zai tsaya ba.

“Wani shaida ya bi direban da ya gudu da babur jim kadan bayan afkuwar lamarin a yankin Oba Ile na Akure.
"Mutanen da lamarin ya faru a kan idonsu sun tabbatar da hakan har da ma iyayen yarinyar da aka buge," in ji shi.
Taswirar Ondom
Yan sanda sun ce motar ayarin matar shugaban kasa ce ta kaɗe yarinya a Ondo ba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ondo ya kai ziyara kai tsaye gidan iyalan marigayiyar domin jaddada cewa za a gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da adalci.

Rundunar ƴan sanda ta yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa yarinyarsu tare da yin kira ga jama’a da su bayar da hadin kai wajen kamo wanda ya aikata laifin, rahoton Punch.

Ta kuma bukaci duk wanda ke da wani bayani da zai taimaka wajen kama direban da ya gudu da ya hanzarta kai rahoto zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da shi.

Yan sanda sun ɗauki mataki a Filato

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ƴan sanda ta ɗauki matakai masu tsauri domin kamo duk mai hanni kan kashe-kashen da suka faru a jihar Filato.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da sufetan ƴan sanda na ƙasa ya kai jihar tare da jajantawa iyalai da ɗaukacin al'umma bisa wannan mummunan lamari.

Ƴan sanda sun kama manyan mutane biyu da ake zargi da hannu a harin da aka kai a Karamar Hukumar Bokkos, kuma tuni bincike ya yi nisa domin gano duka masu hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262