Sarkin Musulmi Ya Gama Shiri, Najeriya Za Ta Zama Ƙasar Musulunci? NSCIA Ta Yi Bayani
- Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa Sultan na shirin musuluntar da Najeriya
- A wata sanarwa da Majalisar ta fitar ranar Talata, ta ce zargin wanda aka jinginawa Mai Alfarma Sarkin Musulmi ba gaskiya ba ne
- Ta buƙaci ɗaukacin ƴan Najeriya su yi fatali da labarin mara tushe balle makama, tana mai rokon jam'a su rika bincike kafin yaɗa jita-jita
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Koli ta Harkonin Addinin Musulunci (NSCIA) ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ana shirin musuluntar da Najeriya.
NSCIA ta karyata raɗe-raɗin wanda ake yaɗawa cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, na yunkurin musuluntar da Najeriya.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin mai ba NSCIA shawara kan harkokin shari'a, Imam Haroun Muhammad Eze ya fitar ranar Talata, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
"Ba ka yi mana adalci ba," NLC ta yi raddi ga Obasanjo kan mafi karancin albashin N70,000
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi na shirin musuluntar da Najeriya?
A cikin sanarwar, Imam Haroun Muhammad, ya bayyana cewa wannan zargi da ake jinginawa mai alfarma sarkin Musulmi ba shi da tushe balle makama.
Ya ce Sultan, wanda ake jinginawa wannan karya, ya yi tafiya zuwa ƙasashen ketare sama da makonni biyu da suka gabata.
Imam Haroun ya ce:
“Hankalin NSCIA ya kai ga wata jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta, wacce ke danganta wani bayani mara daɗi ga Sarkin Musulmi kan batun wai ana kokarin musuluntar da Najeriya.
"Wannan karya ce tsagwaronta, babu wata hujja ko dalili da ke tabbatar da hakan. Bugu da kari, Sarkin Musulmi, wanda ake zargin ya fadi hakan, ba ya ƙasar nan tun sama da makonni biyu da suka gabata.”
Sarkin Musulmi jagoran al'ummar Musulmi ne
Imam Haroun Eze ya bayyana cewa al’ummar Musulmi da sultan ke jagoranta sun kunshi mutane daga kabilu daban-daban a Najeriya.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Ana shirin cafke Sanata Natasha kan jawabin da ta yi a taron IPU? Bayanai sun fito
Don haka a cewarsa, bai dace a danganta shi da irin wadannan kalamai na raba kan al’umma ba.
"Mutum mai cikakken hankali ba zai yi tunanin cewa jagora mai girma da mutunci kamar Sarkin Musulmi zai fadi irin wannan magana mai muni ba," in ji shi.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa, duk da majalisar ba ta yi niyyar mayar da martani ga irin wadannan maganganu marasa tushe ba, amma dole ne ta wayar da kan al’umma domin kada wasu su dauki wannan jita-jita da gaske.
Don haka, Imam Haroun ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da wannan labari kuma su rika tabbatar da gaskiyar kowanne bayani kafin su yarda ko yada shi.
Sultan ya bukaci gyara kudirin haraji
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci (NSCIA) karkashin sarkin Musulmi ta bukaci Majalisar Dattawa ta sake duba wasu wurare a kudirin haraji.
NSCIA ta buƙaci Majalisar ta cire wasu sassa a kudirin harajin saboda sun saɓawa addinai, ta na mai godewa damar da aka ba ta na ba da gudummuwa kan dokokin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng