An Yi Nasarar Murƙushe Riƙakken Ɗan Bindiga bayan Zama Jagora da Yayansa Ya Mutu

An Yi Nasarar Murƙushe Riƙakken Ɗan Bindiga bayan Zama Jagora da Yayansa Ya Mutu

  • Jami'an sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Kachalla Bello Kaura a kauyen Goburawar Dawan Jiya da ke karamar hukumar Anka a Zamfara
  • Kaura da mayakansa sun mutu a wani samame da dakarun Fansan Yamma suka kai cikin mako guda a maboyarsu kamar yadda majiyoyi suka tabbatar
  • Kachalla Kaura ya yi kaurin suna da kai hare-hare a kauyukan da ke Zamfara, Kebbi da Sokoto, kuma yana da alaka da 'yan kungiyar Ansaruddin
  • Bayan rasuwar Shadari, Kaura ya karbi jagoranci, yana kai farmaki a Anka, Bukkuyum, Gummi da kuma yankunan kan iyakar Kebbi da Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Anka, Zamfara - Rundunar sojojin Nageriya na ci gaba da samun galaba kan hatsabiban yan bindiga a jihar Zamfara.

Sojojin Operation FANSAN YANMA sun hallaka wani shahararren shugaban 'yan bindiga, Kachalla Bello Kaura, a wani farmaki da suka kai Goburawar Dawan Jiya.

Kara karanta wannan

Sarakunan Arewa sama da 86 sun yi magana da murya daya kan tsaro

Sojoji sun hallaka ɗan bindiga a Zamfara
Sojojin Najeriya sun shammaci mayaka inda suka hallaka ɗan bindiga a Zamfara. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Asali: Facebook

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa farmakin ya auku ne cikin mako guda, inda Kaura da mayakansa suka mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kona masallacin Juma'a

Wannan na zuwa ne bayan yan bindiga sun yi barna a wasu yankunan jihar Zamfara inda suka lalata dukiyoyin al'umma.

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kona masallacin Juma’a, asibitin kula da lafiya da gidaje fiye da goma a Biyabiki da ke Zamfara.

Hare-haren sun faru ne da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Asabar 12 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ramuwar gayya kan kisan 'yan uwan Adamu Aliero.

Shaidu sun ce ba a yi garkuwa ko kisa ba, amma 'yan bindigar sun kona gine-gine sannan suka tsere bayan kusan awa guda suna barna.

Yadda aka yi ajalin shahararren dan bindiga a Zamfara
Jami'an tsaro sun yi galaba kan yan bindiga bayan hallaka wani shahararre. Hoto: Legit.
Asali: Original

Hare-haren da marigayi ya rika kaiwa Zamfara

Majiyar ta fahimci cewa Kachalla Kaura babban fitaccen dan ta’adda ne da ke da hannu a hare-hare masu yawa a jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto.

Kara karanta wannan

'Dan daba Dujal ya mika wuya bayan kashe mutane da dama a Kano da Jigawa

An ce yana da alaka da kungiyar Ansaruddin, kuma ana zargin ya taimaka musu shiga daji Bagega da Gando don koyon hada bama-bamai.

An haifi Kaura a kauyen Sunke na karamar hukumar Anka, shi ne kanin marigayi Kachalla Alhaji Shadari da jami’an tsaro suka kashe a Sunke.

Bayan rasuwar Shadari a watan Janairun 2023, Kaura ya zama jagora yana kai farmaki a Anka, Bukkuyum, Gummi da kuma sassan Kebbi da Sokoto.

Hukuma ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da matsa lamba ga 'yan ta’adda tare da neman goyon bayan bayanan sirri daga mazauna yankin.

Yadda 'dan bindiga ke bautar da al'umma

Kun ji cewa hatsabibin ɗan bindiga mai suna Kachalla Jiji Dan Auta ya mamaye kauyuka uku a Anka, jihar Zamfara, ya kakabawa mutane bauta.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Yan Yatankari, Yar Sabaya da Birnin Doki, inda mutanen ke yin aikin leburanci a gonakin Ɗan Auta.

Rahotanni sun bayyana cewa Dan Auta ya gargadi mutanen yankin da su dawo ranar Litinin, 14 ga Afrilun shekarar 2024 domin ci gaba da noma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng