Lai Mohammed Ya Bayyana Nasara Mafi Girma Da Ya Samu A Matsayinsa Na Minista A Gwamnatin Buhari

Lai Mohammed Ya Bayyana Nasara Mafi Girma Da Ya Samu A Matsayinsa Na Minista A Gwamnatin Buhari

  • Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce sun cimma nasara a kokarin dawo da kayyakin tarihin da aka sace daga Najeriya
  • Minsistan yace zuwa yanzu sun kammala yarjejeniyar dawo da wasu kayan tarihi sama da dubu da kasashe daban-daban
  • Ministan ya kuma bayyana za a fadada gidan adana kayan tarihi na kasa, don samun damar adana kayan da aka karbo

FCT, Abuja - Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ce babban abin da ma'aikatarsa tayi a bangaren al'adu da yawon bude ido shine dawo da daruruwan kayan tarihi da aka sace.

Mohammed ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a taron bayyana ayyukan shugaba Buhari karo na 26 (2015-2023), rahoton Daily Trust.

Lai Mohammed
Lai Mohammed Ya Bayyana Nasara Mafi Girma Da Ya Samu A Matsayinsa Na Minista A Gwamnatin Buhari. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga

Ya ce:

"Daga lokacin da muka karbi aiki, kokarin dawo da kayyakin tarihin da aka sace daga Najeriya - wanda muka kafa ranar 28 ga Nuwamba 2019 - an samu gagarumar nasara, inda jumallar karfen tagullar Benin 1,130 za su dawo Najeriya daga Jamus kadai.
"An sanya hannu a halattacciyar yarjejeniyar dawo da gaba daya tagullar Benin 1,130 da ke gidajen adana kayan tarihi daban daban a Jamus ranar 7 ga watan Yuli, 2022.
''Tun daga sannan aka fara aikin dawo da kayan inda rukunin farko ya iso Najeriya a Disambar 2022 bisa rakiyar ministan harkokin kasashen waje da al'adu na kasar Jamus da kuma tawagar manyan jami'an gwamnati 80 da ma'aikatan gidajen adana kayan tarihi. Najeriya yanzu ita ce kan gaba a duniya wajen kokarin dawo da kayan tarihi mallakinta."

Mohammed ya kuma ce ma'aikatar sa ta yi nasarar dawo da wata tukunyar kasa mai shekara 600 daga kasar Holan a Oktoban 2020.

Kara karanta wannan

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

Ya kara da cewa an sake gano wasu karafunan tagullar Benin daga Jami'ar Aberdeen da kuma kwalejin Jesus ta Jami'ar Cambridge da kuma babban gidan tarihi, New York.

Har wa yau, ya cigaba da cewa sun sanya hannu a yarjejeniyar dawo da wasu karin tagullar 72 daga gidan adana tarihi na Horniman da ke London a Oktobar 2022.

Mohammed ya ce ma'aiktar sa tana matakin gaba na bada cikakken tsaro ga daruruwan kayan da ta dawo da su daga gidan adana kayan tarihi na Pitt Rivers da ke jami'ar Oxford; gidan adana kayan tarihi na Ashmolean shima a jami'ar Oxford.

Ya kuma ce an kuma dawo da daruruwan kayan da aka kwashe daga gidajen adana kayan tarihi na Archaeology da Anthropology na jami'ar Cambridge; Glasgow City Council a Scotland da kuma gidan adana kayan tarihi na kasar Scotland.

Ministan ya bayyana cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara aikin fadada gidan adana kayan tarihi na kasa, da ke Benin City don adana kayan da aka karbo.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ku Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudadenku, Zamu Bi Umurnin Kotun Koli: Gwamnatin Tarayya

Ya kuma kara da cewa suna duba yiwuwar zamanantar da gidan tarihin masarautar Benin.

Babban nada da ke ci min tuwo a kwarya a matsayin minista, Lai Mohammed

A wani rahoton, Lai Mohammed kuma ya bayyana babban nadama da ke ci masa tuwo a kwarya a matsayin minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel