Yadda Ndume Ya Saka Tinubu a Gaba kan Rashin Tsaro da Wasu Harkokin Mulki

Yadda Ndume Ya Saka Tinubu a Gaba kan Rashin Tsaro da Wasu Harkokin Mulki

A 'yan kwanakin nan, Sanata Ali Ndume ya sake maganganu da dama a kan salon mulkin Bola Tinubu da suka shafi tsaro, raba mukami da sauransu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume na cikin Sanatocin jam'iyyar APC da ba su yin shiru a kan tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu.

A makon da ya wuce, Sanata Ali Ndume ya yi maganganu da suka shafi yadda Bola Tinubu ke raba mukamai da magance matsalar tsaro.

Ndume
Ndume ya bukaci Tinubu ya sauya salon tafiyar da mulki. Hoto: Bayo Onanuga|Senator Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu maganganun da Sanata Ndume ya yi a kan salon mulkin Tinubu da yadda suka tayar da kura a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Maganar Ndume kan rabon mukamai

Yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Ndume ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake ware wasu yankuna daga cikin manyan mukaman da gwamnatin Tinubu ke rabawa.

Sanatan ya bayyana hakan a matsayin sabawa sashe na 14 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ke tanadar da daidaito da wakilci a kowane sashe na ƙasa.

Ndume ya ce:

“Mutum 72 daga cikin waɗanda Tinubu ya ba mukamai Yarabawa ne.
"Ba wai ina magana kan Arewa ko Kudu ba ne kawai, kundin tsarin mulki ya ce kada a bar wani yanki a gefe. Ya kamata kowa ya ji yana da hannu a tafiyar gwamnati.”

Ya ce ya bayyana wannan ne saboda yana zaton Shugaban ƙasa ba shi da masaniya kan yadda aka tafka wannan kuskuren.

Tinubu
Ndume ya zargi Tinubu da nuna wariya wajen rabon mukamai. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Maganar da Ali Ndume ya yi ta dauki hankali a fadin Najeriya har ya kai ga martani daga fadar shugaban kasa.

Fadar shugaban kasa ta ce abin da Ndume ya fada ba daidai ba ne, har ta fitar da adadin mutanen da Tinubu ya nada amma ta gano akwai kuskure a ciki.

Ta ba da hakuri kan kuskuren tare da cewa za ta fitar da sahihin adadi amma dai har yanzu bata fitar ba.

2. Gargadin Ndume kan farfadowar Boko Haram

A wata hira da shi, Sanata Ndume ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye ƙauyuka uku a Borno.

Baya ga haka, ya yabawa Gwamna Babagana Zulum bisa nuna rashin tsoro da kuma fitowa ya bayyana halin da al’umma ke ciki.

A bayanin da ya yi, ya ce:

“Farfadowar Boko Haram a Borno abin damuwa ne. Ina goyon bayan korafin Gwamna Zulum kuma ina kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
"Lokaci ya yi da za a samar da mafita mai dorewa.”

Tribune ta wallafa cewa kiran da Ndume ya yi, bai yi wa Daniel Bwala daɗi ba, inda ya ce Sanata na shi bai kyauta ba.

A cewarsa, Ndume ya gaza kawo sauyi duk da cewa ya shafe fiye da shekaru 20 yana wakiltar jama’ar Borno a majalisa.

Bwala
Bwala ya nuna rashin jin dadin maganar Ndume kan Boko Haram. Hoto: Daniel Bwala|Senator Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

3. Ndume ya bukaci sauke farashin abinci

Sanata Mohammed Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakan gaggawa domin dakile hauhawar farashin kaya da yawaitar rashin aikin yi a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa Ali Ndume ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar daga Abuja ranar Talata, 15 ga watan Afrilu.

Ya kara da cewa irin wadannan matakai na da matukar muhimmanci idan har ana son ‘yan Najeriya su amfana da gyare-gyaren da ake gudanarwa a kasar nan.

Ndume
Ndume ya bukaci Tinubu ya rage farashin abinci. Hoto Senator Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

Ndume ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ayyana dokar ta-baci kan batun abinci, yana mai cewa matakin ya nuna kishin kasa.

Ya ce hakan zai taimaka wajen karfafa samar da abinci a gida da kuma rage tsadar kayan masarufi a kasuwanni.

2027: Tinubu ya hana fara kamfen

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi magana kan wadanda suka fara yi wa Bola Tinubu kamfen din 2027.

Bola Tinubu ya ce har yanzu lokacin fara yakin neman zabe bai yi ba, saboda haka ya yi kira ga magoya bayan shi da su dakata.

Ya kuma bayyana cewa idan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da lokacin fara yakin neman zabe zai sanar da matsayar shi a kan 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng