Sababbin Nade Nade 10 na Shugaba Tinubu da Yankunan da Suka Fito

Sababbin Nade Nade 10 na Shugaba Tinubu da Yankunan da Suka Fito

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fuskanci suka saboda irin zaɓin da yake yi wajen raba muƙamai a gwamnatinsa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wasu mutane da dama na ganin cewa waɗannan naɗe-naɗen nasa sun fi karkata zuwa wasu sassan ƙasar nan fiye da wasu.

Attahiru Jega, Bayo Ojulari
Tinubu ya yi nade-nade a gwamnatinsa Hoto: @aonanuga1956, @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ce sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya zargi Shugaba Tinubu da saɓawa kundin tsarin mulki wajen yin naɗe-naɗen siyasa.

An caccaki Tinubu kan rabon muƙamai

Ya jaddada cewa naɗe-naɗen da Tinubu ya yi tun bayan hawansa kan karagar mulki kusan shekaru biyu da suka wuce, ba su wakilci yankunan Najeriya kamar yadda doka ta tanada ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ndume ya ambaci sashe na 14(3) na kundin tsarin mulki na 1999, wanda ke buƙatar a raba muƙamai cikin adalci tsakanin yankunan ƙasar nan.

Da take mayar da martani, fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da zargin, inda ta bayyana shi a matsayin yunƙurin kawo ruɗani da rarrabuwar kai.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafin X, fadar shugaban ƙasa ta gargaɗi Ndume da ya daina biyewa son zuciyarsa.

Sababbin muƙaman da Tinubu ya naɗa

Biyo bayan hakan, an tattaro jerin muƙamai 10 da Shugaba Tinubu ya naɗa na baya-bayan nan da kuma yankunan da suka fito.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Ayo Sotinrin (Kudu maso Yamma)

Ayo Sotinrin
Bola Tinubu ya ba Ayo Sotinrin mukami Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

A ranar 4 ga watan Afrilu, 2025, an sanar da nada Ayo Sotinrin a matsayin sabon manajan Dldarakta na bankin noma (BOA).

Ayo Sotinrin wanda ya taɓa shugabancin kamfanin SAO Group, yana da ƙwarewa a ɓangaren aikin gwamnati da na kasuwanci.

2. Bashir Bayo Ojulari (Jihar Kwara, Arewa ta Tsakiya)

Bayo Ojulari
Bayo Ojulari ya zama sabon shugaban kamfanin NNPCL Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

A ranar 2 ga watan Afrilu, 2025, Shugaba Tinubu ya amince da naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPCL wanda ya maye gurbin Mele Kyari.

Ojulari wanda ɗan jihar Kwara ne, ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaba kuma babban jami’in gudanarwa a kamfanin Renaissance Africa Energy Company.

3. Ahmadu Musa Kida (Jihar Borno, Arewa maso Gabas)

Har ila yau a ranar 2 ga watan Afrilu, 2025, Shugaba Tinubu ya naɗa Ahmadu Musa Kida, ɗan asalin Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na NNPCL, inda ya maye gurbin Cif Pius Akinyelure.

Ahmadu Musa Kida ya kammala digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya a shekarar 1984.

4. Dr. Ibrahim Yahaya Oloriegbe (Jihar Kwara, Arewa ta Tsakiya)

A ranar 30 ga watan Maris, 2025, an sanar da naɗin Dr. Ibrahim Yahaya Oloriegbe a matsayin shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIA) na tsawon shekaru huɗu.

Dr. Oloriegbe wanda tsohon sanata ne da ya wakilci Kwara ta Tsakiya a majalisar dattawa ta tara, ya yi digirinsa na farko a fannin likitanci a jam'iar Ahmadu Bello (ABU) Zariya.

5. Felix Morka (Jihar Delta, Kudu maso Kudu)

Shugaba Tinubu ya naɗa Felix Morka, kakakin jam’iyyar APC na ƙasa, a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta gidan talabijin na Najeriya (NTA).

Sanarwar naɗin na sa fito ne daga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar 28 ga Maris, 2025.

6. Fatuhu Mohammed Buhari (Jihar Katsina, Arewa maso Yamma)

A ranar 28 ga watan Maris, 2025, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Hon. Fatuhu Mohammed Buhari a matsayin darakta janar na hukumar kula da irin na noma ta ƙasa.

An bayyana naɗin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta fannin noma ta hanyar samar da jagoranci mai ma’ana.

7. Sanata Binta Masi Garba (Jihar Adamawa, Arewa maso Gabas)

Binta Masi Garba
Sanata Binta Masi Garba ta samu mukami a gwamnatin Tinubu Hoto: Binta Masi Garba
Asali: UGC

An naɗa Sanata Binta Masi Garba a matsayin shugabar hukumar gudanarwa ta jami’ar fasaha da kimiyyar muhalli da aka kafa a Iyin Ekiti, jihar Ekiti.

Jaridar Leadership ta ce an sanar da naɗin tsohuwar sanatan ta Adamawa ta Arewa kuma tsohuwar ƴar majalisar wakilai a ranar, 25 ga watan Maris 2025.

8. Matthew Hassan Kukah (Jihar Kaduna, Arewa maso Yamma)

Bishop Hassan Kukah
Tinubu ya ba Bishop Kukah mukami Hoto: Bishop Hassan Kukah
Asali: UGC

Shugaban Tinubu ya naɗa Bishop Matthew Hassan Kukah na Cocin Katolika a Sokoto, a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta jami’ar Kimiyya da fasaha da ke Kachia, jihar Kaduna.

An sanar da naɗin Bishop Kukah, wanda ake sa ran zai kawo gogewa da shugabanci mai kyau, a ranar 17 ga watan Maris, 2025.

9. Fatiu Abiola Arogundade (Jihar Lagos, Kudu maso Yamma)

Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Fatiu Abiola Arogundade a matsayin shugaban jami’ar likitanci da kimiyyar lafiya ta tarayya (FUMMS) da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Farfesa Arogundade, kwararre ne a fannin cututtukan koda, kuma ya taba rike mukamin magatakardan hukumar horar da likitoci ta ƙasa (NPMCN) a Ijanikin da ke Legas.

Naɗin na sa ya fara aiki daga ranar 11 ga watan Maris, 2025.

10. Attahiru Muhammadu Jega (Jihar Kebbi, Arewa maso Yamma)

Farfesa Attahiru Jega
Jega ya samu mukami a gwamnatin Tinubu Hoto: @ProfJega
Asali: Getty Images

Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kuma mai kula da shirin gyaran harkar kiwon dabbobi.

Naɗin na sa wanda aka sanar a shafin statehouse.org a ranar, 7 ga watan Maris 2025, na da nufin inganta fannin kiwon dabbobi da kuma ƙarfafa ci gaban ƙasa.

El-Rufai ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya caccaki salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

El-Rufai ya bayyana cewa tun da Tinubu kan kujerar mulki, Najeriya ta fara samun koma baya ta fannin tattalin arziƙi da tsaro.

Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja, ya kuma zargin shugaban ƙasan da fifita ƴan ƙabilarsa wajen raba muƙamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng